Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

  • Wata mata ta shiga komar ‘yan sanda bayan da ta lakadawa mijinta duka har sai da ta sumar da shi
  • Edwin Ugwu wanda ya shigar da kara a gaban kotu ya bayyana wa kotu yadda matar ke cin zarafinsa
  • Alkalin kotun ta bada belin Ebere akan kudi N100,000 tare da daga sauraren karar har zuwa watan Yuni

Jihar Lagos - Wata mata ta sumar da mijinta bayan ta lakada masa duka a layin Lambe Iluyomade a Ago Okota da ke cikin jihar Lagos.

Mutumin mai suna Edwin Ugwu dan shekara 56 ya labartawa kotun majistare a jihar Lagos yadda matarsa mai suna Ebere ta ke dukansa da zaran ya mata wani laifin da bai kai komai ba.

Matar aure/kotu/dukan miji
Miji ya kwana a asibiti saboda dukar da matar ta masa a Legas: Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Miji ya ce irin azabtar dashi ta take ya yi yawa wanda har ya kai ga lakada masa dukan da ya suma aka wuce dashi asibiti, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bai Bani Lokaci Ba: Dan Haya Ya Maka Mai Gida a Kotu Kan Watsar Da Kayansa

Dan sanda mai gabatar da kara, DSP Kehinde Ajayi, ya ce ma’auratan suna zaune ne a layin Lambe Iluyomade a Ago Okota dake cikin jihar Lagos, sun samu sabani wadda har ya kai ga tashin jijiyoyin wuya kafin matar Edwin ta daka shi wadda ya yi sanadiyyar suma tare da kai shi asibiti don ceto rayuwarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau rahotanni sun tabbatar da cewa matar da ake zargi ta musanta laifukan da ake tuhumarta da shi na cin zarafi da wulakanta dan Adam.

Daga bisani, dan sanda mai gabatar da kara ya nemi kotun da ta bada ranar da za a ci gaba da zaman sauraren wannan karar.

Mai shari’a, Mrs E. Kubeniji ta bada belin wacce ake karan akan kudi N100,000 da shaidu guda 2, sannan ta daga sauraren karar zuwa 6 ga watan Yuni na wannan shekara.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Roki Majalisa Ta Bada Damar Ya Karbo Aron $800m a Karshen Mulkinsa

Dan Haya Ya Maka Mai Gida a Kotu Kan Watsar Da Kayansa

A wani labarin, jaridar Legit Hausa ta bada rahoton cewa an maka wani mai gidan haya a kotu bisa zargin cin zarafin wani mai haya a gidansa, mai gidan ya watsar da kayan mai hayan ne a layi ba tare da bashi lokacin tashi ba.

Ana tukumar mai gidan da laifuka 4 da suka hada da daukar doka da hannu da cin zarafi da kuma yin sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel