Abin Takaici: Mata Ta Dawo Da Ciki Bayan Zuwa Wurin Alkali Don Ya Raba Auren

Abin Takaici: Mata Ta Dawo Da Ciki Bayan Zuwa Wurin Alkali Don Ya Raba Auren

  • Wata mata da ta garzaya wurin alkali don ya raba aurenta da mijinta a karshe ta dawo da juna biyu har na tsawon wata biyu
  • Ma’auratan sun sha fama a baya na matsaloli daban-daban inda suka yanke hukuncin zuwa wurin alkali don ya raba auren
  • Amma sai ga shi matar ta bayyana da juna biyu, ashe duk tsawon wannan lokaci suna haduwa duk karshen sati

Wata mata da takai karan mijinta kotu don alkali ya raba aurensu, a karshe ta dawo da ciki wanda mijin da take son rabuwa dash din ya dirka mata.

Ma’auratan, a baya sun sha fama da matsaloli daban-daban wanda hakan ya sa suka yanke hukuncin zuwa don raba auren ko ya huta.

man/woman
The Couples, Hoto: Carlos Pintau
Asali: Getty Images

An ruwaito cewa matar ta bar gidan mijin na tsawon lokaci don ta huta saboda matsalolin da suke fama da su.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Ake Bada Kwangilolin Biliyoyi a Karshen Mulkinmu – Gwamnatin Buhari

‘Yan uwa da abokan arziki sun yi kokarin sasanta su akan rikicin nasu amma suka ki sauraronsu, damuwarsu kawai shine a raba auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin wadanda suke kokarin sasanta su sun cika da mamaki bayan sun fahimci cewa ai matar na dauke da juna biyu har na tsawon wata biyu.

Daga baya ne aka fahimci cewa ashe lokacin da matar ta fice daga gidan mijin, sukan kadu a wani wurin da ta koma har hakan ta faru.

Da take yada wa a shafinta na Twitter, Chinaza ta ce:

“Hhhh kamar wasa, matar nan ta bar gidan miji lokacin hatsaniya, ashe mijin na zagawa su hadu a karshen sati.”

Ma’auratan har yanzu da aurensu, an haifi jaririn har an rada masa suna a majami’a.

Mutane masu ta’ammali da shafin Twitter sun tofa albarkacin bakinsu

Kara karanta wannan

Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

@Unjoerated:

“Mahaifyata ta taba ce min fada tsakanin ma’aurata ba ya kai haka, bayan kitimurmurar, fadan zai ci gaba.”

@Logiebo1:

“Yanzu na koyi darasi, kar ka kuskura ka shiga rikicin ma’aurata.”

@the_drterry:

“Kawata ta yi haka, naji dadi yanzu ta koma ga mijinta, har ta sami ciki tana tsammanin haihuwa nan kusa.”

Budurwa ta Fashe da Kuka Bayan Shafe Makwanni 3 ba Ciniki

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya ta fashe da kuka saboda ta shafe akalla makwanni uku babu ciniki a shagon.

Budurwar wadda take siyar da kayan kawa, ta zaga shagon tana hawaye saboda rashin ciniki duk da karya farashi da ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel