Hukumar Hisbah a Kano Ta Gargadi Masu Adaidaita Sahu Kan Manna Hotunan Badala

Hukumar Hisbah a Kano Ta Gargadi Masu Adaidaita Sahu Kan Manna Hotunan Badala

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gargadi masu adaidaita sahu kan manna hotunan badala da suke yi a abin hawansu
  • Sheikh Harun Ibn Sina, kwamandan hukumar ne ya yi wannan gargadi a ofishinsa inda ya ja kunnen masu aikata hakan
  • A karshe ya ce wadannan abubuwa sun sabawa koyarwar addinin Musulunci da tsarin zamantakewa na al’ummar jihar

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta koka kan yadda masu adaidaita sahu a jihar ke manna hotunan batsa ko wasu abubuwa da ke bata tarbiyyar al’umma wanda ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.

Kwamandan hukumar, Sheikh Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ga ‘yan jaridu a ofishinsa, inda ya gargadi masu adaidaita sahun da su kaucewa duk wani abu da zai gurbata tarbiyya.

hisbah
Kwamandan Hisbah, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Hukumar Hisbah ta dade tana yaki da gurbacewar tarbiyya a jihar da wadanda suka sabawa koyarwar addinin Musulunci da kuma al'adun Hausawa don ganin an dakile barna.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane

Rahotanni sun tattaro cewa hukumar ta Hisbah na kokarin ganin ta gyara tarbiyya na matasa da ya yi katutu a cikin jihar, musamman masu yada bidiyon TikTok na batsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanin kwamandan hukumar Hisbah

“Mun samu bayanai cewa masu adaidaita sahu suna aikata laifuka kamar guda 3 da suka sabawa tsarin Musulunci”.
“Na farko, suna kunna wakoki kuma su kure sautinsu da ke damun har mutanen da ke gefe, na biyu suna manna hotunan batsa wanda bai dace ba ko dadin kallo, na uku suna shiga wanda ya sabawa al’adunmu da kuma tsarin addininmu, bayan kuma daukan mata da suke a matsayin fasinjojinsu”.
“Wadannan abubuwa sun sabawa koyarwar Musulunci, muna yi musu gargadi da su kiyaye wadannan abubuwa, in kuma suka ki to tabbas za mu dauki matakai, ba za mu bar irin wannan ya ci gaba a jihar Kano ba, ya kamata suji tsoron Allah su bar aikata hakan”.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An sace shugaban karamar hukuma a Arewa, an kashe dan sandan bayansa

Hukumar Hisbah a jihar Kebbi Sun Kama Samari da Yan Mata Suna Holewa a Otal

A wani labarin, Jami'an rundunar 'yan Hisbah a jihar Kebbi sun kama wasu matasa maza da mata har 12 suna aikata baɗala a wani Hotel cikin birnin Kebbi.

Kwamandan rundunar 'yan Hisbah na Kebbi, Ustaz Suleiman Muhammad, ya tabbatar da haka ne yayin zantawa da yan jarida ranar Alhamis a Birnin Kebbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel