Babbar Nasara: Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna

Babbar Nasara: Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna

  • Hukumar yan sanda a jihar Kaduna ta ce jami'anta sun yi nasarar tura wani kasurgumin ɗan bindiga zuwa lahira
  • Kakakin yan sanda, Muhammad Jalige, ya ce dakarun sun yi artabu da tawagar yan bindiga a Kidandan, yankin Giwa
  • Kwamishinan yan sanda ya yaba wa kwazon dakarun, ya roki su ci gaba da haka kan ayyukan yan bindiga a Kaduna

Kaduna - Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce jami'anta sun samu nasarar kashe kasurgumin ɗan bindigan jeji, wanda ya addabi mutane a jihar.

Bayan halaka ɗan ta'addan, dakarun 'yan sanda sun kwato Babur ɗin da suke amfani da shi a ƙauyen Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa, a Kaduna.

Jami'an yan sanda.
Babbar Nasara: Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna Hoto: Policeng
Asali: UGC

Rahoton Punch ya ce Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan, DSP Mohammed Jalige, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

Jalige ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yau (Lahadi) 7 ga watan Mayu, 2023 da misalin karfe 10:30 na safe, dakarun yan sandan da suka fita sintiri a kan Titin Fatika, suka ci karo da tawagar yan bindiga a kan Babura, sun yi shigar Sojoji."
"Nan take gwarazan jami'an yan sanda suka tarbe su, aka yi musayar wuta kuma sun nuna wa yan bindigan ruwa ba sa'an kwando bane. Sun sheƙe ɗaya daga cikin yan bindigan wanda ya sanya kakin soji."
"Sauran yan bindigan suka ari na kare ɗauke da muggan raunukan harsashin bindiga, haka nan jami'an sun kwato Babur ɗin da maharan ke amfani da shi."

A cewarsa, jami'an yan sanda ba su kwanta ba, sun kara tsananta sintiri a kan Titin domin dakile duk wani hari da yan ta'addan ka iya ƙara yunkurin kaiwa.

CP ya yabawa dakarun bisa kwazon da suka nuna

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Jalige ya ƙara da cewa kwamishinan 'yan sanda a Kaduna, Musa Garba, ya jinjinawa kwazon da dakarun suka nuna wanda ya basu wannan nasara.

Ya ce kwamishinan ya roki jami'an kar su gajiya su ɗora daga nan kan yan bindigan jeji da sauran muggan laifuka a jihar Kaduna, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Sojoji sun ceto ma'aikatan NGO

A wani labarin kuma Dakarun Soji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai da Yan Ta'adda Suka Sace a Borno

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da ma'aikatan kungiyar NGO biyu daga cikin uku, waɗanda 'yan ta'addan ISWAP suka yi garkuwa da su a jihar Borno.

Har yanzun 'yan ta'addan na rike da ragowar mutum uku, waɗanda suka sace daga gidan baƙi na kungiyar kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel