Shugaba Buhari Ya Sabunta Wa'adin Shugabancin Yan Majalisar Amintattu Na NPTF

Shugaba Buhari Ya Sabunta Wa'adin Shugabancin Yan Majalisar Amintattu Na NPTF

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sabunta wa'adin shugabancin yan majalisar amintattu na Asusun kula da harkokin yan sanda
  • Wannan shine wa'adin mulkinsu na karshe inda za su shafe tsawon shekaru uku kuma zai fara aiki daga ranar 19 ga watan Mayu
  • An sabunta mukamin ne saboda gagarumin kokarin da suka yi wajen inganta tsaron cikin gida a kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabonta mukaman mambobin kwamitin amintattu na Asusun Kula da Harkokin 'Yan Sanda (NPTF) na shekaru uku wanda zai yi daidai da wa'adinsu na karshe.

Ma'aikatar kula da harkokin 'yan sanda ta bayyana a ranar Juma'a, 5 ga watan Afrilu, cewa sabbin nade-naden zai fara aiki daga ranar 19 ga watan Mayu, kamar yadda dokar NPTF na 2019 ta tanadar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Yan Kwanaki Kafin Mika Mulki: Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Ta kara da cewar nadin ya biyo bayan gagarumin kokarin da kwamitin ya yi kamar yadda aka gani wajen karfafa tsaron cikin gida a Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara Kan Kujerar Kakakin Majalisa

Sunayen mambobin majalisar NPTF

An fara nada mambobin kwamitin ne a watan Mayun 2020 na tsawon wa'adin shekaru uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda aka nadan sune; Mista Suleiman Abba, shugaban kwamitin da kuma Mista Abdullahi Bala, babban sakatare da kuma wakilan ma'aikatun harkokin yan sanda, shari;a da na kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa.

Sauran sune Mista Mansur Ahmed, yana wakiltan ma'aikatu masu zaman kansu, Mista Michael Adebiyi, yana wakiltan kungiyoyin jama'a da Sufeto Janar na yan sanda, yana wakiltan rundunar yan sandan Najeriya.

Gwamna Tambuwal ya nada sabbin sakatarori da manyan daraktoci yan kwanaki kafin mika mulki

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya nada sabbin sakatarorin din-din-din 23 da kuma manyan daraktoci 15 yan kwanaki kafin mika mulki.

Gwamna Tambuwal zai mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Bayan Dogon Lokaci, Gaskiya Ta Bayyana Kan Baiwa Kwamishinan Zaben Adamawa Cin Hancin N2bn

Daga cikin wadanda gwamnan ya nada harda babban hadiminsa da daraktan labarai na ofishin mataimakin gwamna Abdulnaseer Abubakar Sayinna da Aminu Abubakar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago na jihar suka koka kan rashin tura wa kungiyoyin kwadago da na hadin gwiwar ma'aikata kudaden da ake cirewa daga albashin ma’aikatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel