Jama’a Sun Shiga Yar Tsere Yayin da Gobara Ta Tashi a Wajen Shagalin Bikin Aure, Bidiyon Ya Yadu

Jama’a Sun Shiga Yar Tsere Yayin da Gobara Ta Tashi a Wajen Shagalin Bikin Aure, Bidiyon Ya Yadu

  • Ba a kare wani bikin aure ta dadi ba a Lagas bayan gobara ta tashi ana tsaka da shagali
  • Mahalarta bikin sun tarwatse don neman mafaka dannan da dama sun tsere yayin da gobarar ta dunga yaduwa a wani bidiyo da ya bayyana
  • Jama'a sun yi cece-kuce kan lamarin yayin da wasu suka daura alhakin abun da ya faru kan wanda ya tsara bikin, wasu kuma sun ce sihiri ne

An samu tashin gobara a wajen wani shagalin bikin aure da aka yi a jihar Lagas a ranar Asabar, 8 ga watan Afrilun 2023.

Shafin LIB ya rahoto cewa gobarar ta barke ne lokacin da ake jawabin fatan alkhairi ga ma'auratan. Lamarin ya afku ne a Yard 158, wani wajen taro a Oregun, Lagas.

Gobara ta tashi a wajen biki
Jama’a Sun Shiga Yar Tsere Yayin da Gobara Ta Tashi a Wajen Shagalin Bikin Aure, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @mamakiing
Asali: TikTok

Wani bidiyo da ke nuna wajen da gobarar ta tashi ya hasko mahalarta bikin suna tserewa yayin da wani da ake ganin MC ne ya bukaci kowa ya yi waje.

Kara karanta wannan

Assha: Wani ya jawo cece-kuce yayin da ya ja akuya a waje shi kuwa yana cikin bas

An gano wasu mutane suna amfani da abun kashe gobara wajen kashe wutan da ya lakume kayan alatun da aka kawata wajen da shi daga sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba a tabbatar da ko mutane sun jikkata ba a wajen. Lamarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@delasotv1 ta ce:

"Mutanen Afrika ba za su taba yarda cewa wannan ba aikin mayu bane idan har suna farin ciki, Kawai akasi aka samu na na'ura...Amma ba za su yarda ba,, abu na farko da zai zo zuciyar uwar matar shine cewa na fadawa diyata kin tabbatar da mutumin nan."=
"Yadda kunnen nan nasa ke lankwashewa, sannan idan uwar matar ta fito ne daga cocin mountain of fire ko chosen mople, toh ba za a taba yin auren nan ba saboda Ubangiji ya amsa da wuta."

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda makaho ya shige soyayya da tsaleliyar budurwa, ya nemi aurenta

@danieludehdante ya ce:

"Wanda ya shirya taron nan shine ya haddasa wanna. Abun bakin ciki ne a rana mafi muhimmanci a garesu. Toh, ku cire damuwa ku yi murnar cewa kun yi aure, Mu bibiyi shafin juna kuma zan bi duk wanda ya yi 'like' din martanina."

Bidiyon yar lukuta da ta yi wuff da angonta dan tsurut

A wani labarin kuma, wata katuwar mata yar Najeriya ta nunawa duniya sahibinta dan tsurut inda ta saki hotunansu na baya da kuma na aurensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel