“Sun Yi Kaman Uwa da ‘Da”: Bidiyon Shirgegiyar Mata Da Masoyinta Ya Yadu

“Sun Yi Kaman Uwa da ‘Da”: Bidiyon Shirgegiyar Mata Da Masoyinta Ya Yadu

  • Sauyawar ban mamaki da wasu masoya biyu da suka dade suna soyayya suka yi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Matar wacce a yanzu ta zama katuwa ta tuna yadda mahaifinta ya nuna adawa da soyayyarsu sannan ya fatattaki sahibinta
  • Bayan shekaru, masoyan sun kasance tare da junansu inda a yanzu suka shige daga ciki a matsayin mata da miji

Wata shirgegiyar mata yar Najeriya, Mimi Christabel, ta garzaya soshiyal midiya don nunawa duniya mijinta yayin da yi waiwaye zuwa lokacin da suke soyayya.

Mimi ta wallafa tsohon hoton da ta dauka tare da sahibinta, tana mai cewa soyayyarsu na kan hanya madaidaiciya tun daga yarintarsu.

Katuwar mata da mijinta dan tsurut
“Sun Yi Kaman Uwa da ‘Da”: Bidiyon Shirgegiyar Mata Da Masoyinta Ya Yadu Hoto: @christabelmimi
Asali: TikTok

Ta tuna yadda mahaifinta ya fatattaki sahibinta da kuma yadda mnahaifiyarta ta kusa ba hammata iska da shi.

Ta raka wallafar tata da wasu kyawawan hotuna wanda ake ganin na kafin aurensu ne sannan ta rufe da wani bidiyo na daurin aurensu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda makaho ya shige soyayya da tsaleliyar budurwa, ya nemi aurenta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane da dama sun yi mamakin yadda suka ta tashi daga yar siririya zuwa shirgegiyar mata yayin da mutumin ke nan a yadda yake dan tsurut da shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@iam_Mary ta ce:

"Amma sun yi kama da uwa da 'da mana."

@opeyemisinger2 ya ce:

"Gayen ya ki ya girma."

@Shuga_Lee ya ce:

"Kin tabbata wannan gayen shine wannan...Ko dai ke yarinyar nan baki basa abinci ne."

@imose_adams ya ce:

"Karamin jiki ba cuta bace mutane na yanke hukunci kan abun da basu sani ba idan mutumin nan ya fada maku yana da shekaru ba za ku yarda ba."

@user3796362859082 ya ce:

"Ina tayaki murna amma hajiya ki sauya hoton shafinki yanzu ke matar aure ce."

@oyarebumunir ya ce:

Kara karanta wannan

“Sun Yi Kokarin Kashe Mani Aure”: Matashiya Ta Raba Gari Da Danginta Bayan Ta Auri Dan Najeriya

"Abun da Allah madaukakin sarki ya kaddara: babu namiji ko macen da za ta iya karya shi; Allah abun godiya; dukkanmu muna rokon samun kyakkyawan karshe."

Bidiyon makaho da ya nemi auren wata tsaleliyar budurwa ya bar mutane baki bude

A wani labarin kuma, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wani makaho da ya nemi auren wata tsaleliyar budurwa.

Matashiyar dai ta kasance aminiya ga makahon wanda kyautatawar da take yi masa ne yasa ya nemi aurenta a bainar jama'a a wajen sana'arta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel