‘Saboda Me’: Yadda Jama’a Suka Yi Mamaki Yayin da Makaho Ya Nemi Auren Tsaleliyar Budurwa

‘Saboda Me’: Yadda Jama’a Suka Yi Mamaki Yayin da Makaho Ya Nemi Auren Tsaleliyar Budurwa

  • Wata kyakkyawar budurwa ta gaza yarda da abun da idanunta suka gani yayin da amininta mai lalurar makanta ya nemi ya aure shi a kasuwa
  • Ya zo da abokinsa da kuma wani shahararren dan TikTok don ayyana kudirinsa amma dai abun bai yi wa budurwar dadi ba sosai
  • Bayan ta tsere daga shagonta da farko, matashiyar ta sake dawowa wajen don amincewa da bukatarsa cikin yanayi mai tsuma zuciya

Wani dan Najeriya mai lalurar makanta ya haddasa cece-kuke a kasuwa yayin da ya nemi auren aminiyarsa cikin yanayi na bazata.

Obinna ya ce ya san Juliet kafin ya makance kuma cewa sun shafe tsawon shekaru biyar suna abota.

Lokacin a ta shiga matsalar rashin muhallin zama, shi da kansa ya bukaci ta dawo gidansa da zama inda ita kuma ta dungi kula da shi.

Kara karanta wannan

“Sun Yi Kokarin Kashe Mani Aure”: Matashiya Ta Raba Gari Da Danginta Bayan Ta Auri Dan Najeriya

Yadda makaho ya shige kogin soyayy
Makaho ya nemi soyayya ana zaune kalau | Hoto: @theoayoms
Asali: UGC

Bayan ya tuntubi shahrarren dan TikTok Theo Ayomoh, Obinna da abokinsa Hemes sun fito don ba Juliet mamaki a kasuwa inda take aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da zuwansu wajen, Obinna ya yi godiya ga Juliet kan kasancewarta aminiya tagari sannan ya bijiro mata da maganar aure.

A bidiyon TikTok din, Juliet ta gudu ta bar shagonta yayin da ta samu labarin cikin kaduwa. Ta fadama Theo cewa bata so yadda bai sanar da ita ba kafin zuwan abun.

Bayan dan lallashi, ta dawo don karbar zoben Obinna, lamarin da ya yi wa mutane dadi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@Adebayo poush ya ce:

“Wasu lokutan mata mafi alkhairi gareku ba lallai ya zo a yanayin abun da kuke so ba amma kada ku kori ni’ima da mijinku saboda yanayin yadda yake.”

Kara karanta wannan

“Kasuwa Bata Yi Mun Dadi Ba”: Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Faduwa Da Ya Yi a Zaben Sanata

@Alexi Atanga ya ce:

“Allah Ubangiji ya ci gaba da tallafa maku sannan ya baku kyawawan yara, ya kamata duniya ta tallafa masu.”

@Emma Juliet276 ta ce:

“Juliet Allah ya yi maki albarka saboda wannan farin cikin, Allah ka taimaka ka dawo masa da ganinsa.”

@fauziatagoe842 ta ce:

“Na yi kuka Allah ya saukaka radadin duk wata zuciya da ke shan wahala a fakaice sannan ya yi maki albarka yar’uwata ya kuma kareku.”

A wani labarin, budurwa ta fusata yayin da saurayinta ya yi mata wata kalar tarba a lokacin da ta kai masa ziyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel