Cece-Kuce Yayin da Wani Mutum Ya Daure Akuya a Wajen Mota, Shi Kuwa Ya Shiga Ciki Yana Jan Ta

Cece-Kuce Yayin da Wani Mutum Ya Daure Akuya a Wajen Mota, Shi Kuwa Ya Shiga Ciki Yana Jan Ta

  • Wani dan Najeriyan da aka hana ya shiga da akuyarsa cikin mota bas ya jawo cece-kuce yayin da ya samo hanyar tafiya da dabbar tasa
  • A wani hoton da ya yadu, an ga lokacin da mutumin ke cikin mota, amma ya leko ta waje yana rike da igiyar da ya daure akuyarsa a jiki
  • Mutumin dai a zahirance daure akuyar ya yi, ya shiga mota tana tafiya yayin da akuyar ke bin motar a waje shi kuwa yana rike da iygar a wuyanta

Wani dan Najeriya ya gano hanya mai ban dariya na isa gida tare da akuyarsa wacce aka hana shi shiga mota bas da ita.

A wani hoton da ya yadu a kafar sada zumunta, wanda Kanife Machienti ya yada a Facebook, an ga mutumin ya daure akuyar ta wajen mota, shi kuwa yana ciki.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda makaho ya shige soyayya da tsaleliyar budurwa, ya nemi aurenta

A lokacin da motar ta fara motsi, wannan zai sanya akuyar arcewa da gudu, lamarin da ya ba mutane da yawa dariya.

Yadda mutum ya dauko akuya a mota, yana jan ta a waje
Hoton yadda mutumin ke jan akuya a mota | Hoto: @kanifemachienti
Asali: Facebook

Wasu kuma sun yi martani da cewa, akwai yiwuwar a sace akuyar kafin mutumin ya isa inda yake son zuwa da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli hoton a nan:

Martanin jama’a

Bayan yada hoton a Facebook, Legit.ng ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa game da hoton:

Paul Uche:

"Martanin wasu mutane dai na ban dariya. Kuna cin nama amma kuna ihun ana cin zarafin dabba. Ta yaya kuke tunanin ake samar da naman? Ta hanyar yiwa dabbobin wakar kumbaya har su sadudu su zama tsinken tsire?’

Kunle Rabiu:

"Wannan ai mugunta ne.”

Hymar David:

"’Yar karamar motsa jiki.”

Dinma Ebae:

"Lallai kam. Wahala kafin mutuwa kenan.”

Daniel Ozioma:

Kara karanta wannan

"Kan 300k": Yadda Uba Ya Gwada 'Yarsa Don Ya Gane Ko Tana Taba Sana'ar Karuwanci a Makaranta

"Ban san me zance ba kuma...wannan ba daidai bane gaskiya. Idan ka ci akuyar kuma sai me kenan? Muna kashe akuya ne kai tsaye. Ba ma wahalar da ita kafin kashe ta ko kuma mu sanya ta gudun tsere da igiya a wuyanta. Abin dariya ne amma kuskure ne.”

Augustgold Nchedo:

"Wannan akuyar za ta fadi hanyar garinsu.”

A wani labarin kuma, wani matashi ne ya yi abin kirki, inda ya dawo wurin matar da ya taba yi mata sata, ya ba ta kyauta kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel