Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Plateau Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar

Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Plateau Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar

  • Nentawe Yilwatda ɗan takarar gwamnan jihar Plateau a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yayi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar
  • Yilwatda yayi zargin cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tafka maguɗi a zaɓen
  • Ɗan takarar ya nuna ƙwarin guiwar sa kan cewa za su kwato haƙƙin su inda yayi kira ga magoya bayan sa da kada su zagi kowa

Jihar Plateau- Ɗan takarar gwamnan jihar Plateau a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Dr Nentawe Yilwatda, yayi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar. Rahoton Daily Trust

Ɗan takarar na jam'iyyar APC ya sha kashi a hannun zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Barista Caleb Mutfwang na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya samu ƙuri'u mafi yawa a zaɓen.

Nentawe
Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Plateau Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yilwatda yayi fatali da nasarar da jam'iyyar PDP ta samu ne a ranar Litinin da yamma lokacin da yake yiwa magoga bayan sa jawabi a Jos babban birnin jihar. Rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

Bayan Shan Kashi a Zaben Gwamna, Dan Takarar APC Yayi Wani Muhimmin Abu Daya Rak

Yilwatda yayi zargin cewa jam'iyyar PDP ta tafka magudi a wasu wurare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

“Zaɓe muka yi na gaskiya. Ba muyi maguɗi a ko ina ba. A ƙananan hukumomi biyu sun bamu tazarar 100,000. Mun sanar da cewa ba a samu fitowar masu kaɗa ƙuri'u ba sosai amma kuma ƙuri'un sun ƙaru fiye da kaso 30%.
"Ta yaya rashin fitowar masu kaɗa ƙuri'u ya rikiɗe zuwa yawan masu kaɗa ƙuri'u. Sai mun kwato haƙƙin mu. Ina da tabbaci, ban karaya ba. Muna da gaskiya a cikin zukatan mu."

Ɗan takarar na APC ya kuma yi kira ga magoya bayan sa da kada guiwoyinsu su sare sannan kada su ci mutuncin kowa.

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

A wani labarin na daban kuma, wasu ƴan takarar gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shirya zuwa kotu domin neman karɓe nasarar da aka samu a kan su.

Ƴan takarar dai sun nuna rashin amincewar su da sakamakon zaɓen gwamnoni a jihohin da suka yi takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel