Yanzu-Yanzu: Daga Karshe Gawuna Yayi Magana Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kano

Yanzu-Yanzu: Daga Karshe Gawuna Yayi Magana Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kano

  • Ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Gawuna, yayi magana kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar
  • Gawuna yace hukumar zaɓe ta INEC ta yi kuskure a wajen bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar
  • Jam'iyyar APC a jihar ta ba INEC wa'adin kwana 7 da ta sake yin duba kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar

Jihar Kano- Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasir Gawuna, yace bayyana yadda yakamata ace sakamakon zaɓen gwamnan jihar ya kasance.

Nasir Gawuna ya bayyana cewa kamata yayi ace hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba wato 'inconclusive'. Rahoton Daily Trust

Yayin da yake jawabi ga ƴan jarida, Gawuna wanda yake tare da shugabannin jam'iyyar APC, yace lamarin akwai ɗaure kai yadda INEC ta bayyana wasu zaɓukan ƴan majalisun dokokin jihar a matsayin 'Inconclusive'.

Kara karanta wannan

Da Sake: Dan Takarar Gwamnan APC Yayi Fatali Da Sakamakon Zabe, Yasha Wani Babban Alwashi

Gawuna ya kuma yi kira ga magoya bayan jam'iyyar su da cigaba da haƙuri duk da irin takalar da za ayi musu. Sannan ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyin su a dalilin rikicin da ya ɓarke a ranar zaɓe da bayan zaɓen.

Gawuna ya kuma nuna ƙwarin guiwar sa kan cewa hukumar INEC za tayi abinda ya dace ta hanyar tabbatar da cewa taba mutane abinda suka zaɓa.

APC ta ba INEC wa'adi

A nata ɓangaren jam'iyyar APC ta jihar ta ba hukumar zaɓen jihar wa'adin kwana 7 da ta tabbatar ta sake duba sakamakon gwamnan jihar da ta bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar ta hannun lauyan ta Abdul Fagge, tace baturen zaɓen jihar ya saɓawa sabuwar dokar zaɓe ta hanyar bambanta zaɓen da aka soke a dalilin rikici da wanda aka soke a dalilin aringizon ƙuri'a, da yadda tayi amfani kawai da na ƙarshen wajen yanke tazarar da aka samu a zaɓen.

Kara karanta wannan

Duka Biyu: 'Yan Daban Siyasa Sun Farmaki Hedikwatar Jam'iyyar APC Bayan Dan Takarar Su Ya Ci Zabe

Fagge yace an karɓi katin zaɓe 273,442 a yankunan da aka soke zaɓe a dalilin rikici da aringizon ƙuri'a, yawan da a cewar sa tazarar (128,897) da aka yi amfani da ita wajen bayyana Abba Kabir Yusuf matsayin wanda ya lashe zaɓen tayi kaɗan a hurumin sabuwar dokar zaɓe.

Siyasa Babu Gaba: ‘Dan takara ya Taya Abba Kabir Yusuf Murnar Karbe Gwamnati a Kano

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Kano, ya karɓi ƙaddara ya taya abokin hamayyar sa da tiƙa shi da ƙasa murnar lashe zaɓe.

Sha'aban Sharada wanda yayi takarar gwamnan jihar Kano, ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Action Democratic Party (ADP), ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a zaɓen sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel