Soja Ya Harbi Dan Achaba, Ya Kashe Mai Jego Da Jinjirinta Kan N200

Soja Ya Harbi Dan Achaba, Ya Kashe Mai Jego Da Jinjirinta Kan N200

  • Al'ummar garin Babanna da ke jihar Neja sun ga wani abun tashin hankali a ranar Litinin da ta gabata
  • Wani jami'in soja ya bindige wani dan achaba inda alburushi ya fita ya samu fasinjar da ya dauko da danta da ke goye kuma sun mutu nan take
  • Rikicin ya samo asali ne bayan da dan achaban ya ki ba sojojin da suka tsare hanya cin hancin N200

Niger - Rahotanni sun kawo cewa wani soja ya harbi dan achaba da wata mai jego da da danta da ya goyo a bayansa a garin Babanna da ke karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Litinin lokacin da mutanen ke hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar mako da ke ci a garin Babanna.

Kara karanta wannan

Kaico: Dan Boko Haram ya ce ya tuba, ashe dashi ake hada baki a farmaki sojoji, ya shiga hannu

Jami'in soja rike da bindiga
Soja Ya Harbi Dan Achaba, Ya Kashe Mai Jego Da Jinjirinta Kan N200 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An tattaro cewa sojan ya harbi dan achaban ne saboda ya ki bashi cin hancin N200 da ya bukata sannan sai harsashin ya fita ta cikinsa ya kuma samu matar da yake goye da Ita da kuma jinjirin da ke bayanta.

Yadda al'amarin ya faru daga bakin mazauna yankin

Wani mazaunin yankin, Saidu Babanna ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daya daga cikin sojojin da aka turo Babanna don kare rayuka da dukiyoyi ya harbi mutum uku saboda cin hancin N200. Lokacin da mutanen ke hanyar shigowa Babanna da safe, sojoji sun karbi N200 daga hannunsu a shingen bincike, sannan da za su koma Nigangi da ke juhuriyar Benin, sojojin sun bukaci su sake biyan N200 wanda suka gaza biya.
"Wannan ne ya yi sanadiyar da wani soja ya bude wuta inda ya kashe mutum uku a kan babur nan take."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Lamarin ya afku ne a yammacin ranar Litinin. Kasuwar Babanna na ci a ranar Litinin. Mutanen da abun ya ritsa da su na hanyar komawa gida daga kasuwa. Lokacin da suke zuwa da safe, akwai sojoji da yawa a kan iyakar jumhuriyar Benin wadanda suka tsayar da su sannan suka karbi N200 a hannunsu.
"Don haka da suke dawowa sojojin sun sake tsayar da su suka bukaci su biya N200 wanda dan achaban ya ki basu. Sai suka fara jayayya sannan dan achaban ya tayar da mashin dinsa sai wani soja ya ta da babur shima ya bisa har ya sha gabansa. Sai ya harbe shi inda harbin ya billa ta cikin dan achaban ya samu matar da yake goye da ita, inda nan take matar da danta suka mutu."

Ya ce an kama sojan sannan an kai shi sashin Bataliya ta 221 da ke Kainji, New-Bussa a karamar hukumar Borgu bayan kiran hukumomin sojoji da hakimi ya yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke a jihar Arewa, an harbe 'yan sanda 2 a hedkwatar INEC

Har ila yau, ya ce matar da danta sun mutu nan take yayin da dan achabar ke samun kulawar likitoci a wani asibiti a jumhuriyar Benin.

Martanin yan sanda

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai cimma nasara ba.

Sai dai kuma, shugaban karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, Alhaji Suleiman Yarima, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa matar da danta sun mutu nan take yayin da dan achaban ya rayu kuma yake samun kulawar likitoci a Parakou, Jumhuriyar Benin.

Ya ce:

"Wadanda abun ya cika da su yan jumhuriyar Benin ne, wadanda suka zo kasuwar Babanna da ke ci duk mako don yin siyayya. An kwashi gawarwakin zuwa jumhuriyar Benin amma ba zan iya tabbatar da jana'izarsu ba a yanzu. Sai dai ana gudanar da bincike."

A wani labari na daban, mun ji cewa dakarun sojoji sun ceto iyalai da masu taimakawa mayakan Boko Haram su 900 a dajin Sambisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel