Yadda Tubabben Dan Boko Haram Ya Kitsa Farmaki Kan Sojoji, 3 Sun Mutu, 4 Sun Jikkata

Yadda Tubabben Dan Boko Haram Ya Kitsa Farmaki Kan Sojoji, 3 Sun Mutu, 4 Sun Jikkata

  • Sojojin Najeriya sun kama wani rikakken tsohon dan Boko Haram da ake zargi da hada kai da tsoffin abokansa
  • Rahoto ya bayyana yadda wannan dan ta’adda ya mika wuya a baya, amma yake kitsa hari kan sojoji
  • Tun farko, ana ci gaba da dasa ayar tambaya game da sahihancin tuban ‘yan ta’addan Boko Haram

Borno, Najeriya - Jami’an rundunar Operation Hadin Kai sun titsiye wani mai suna Ba’ana Bdiya da aka ce tubabben dan ta’addan Boko Haram ne bisa zargin hannu a dasa wani bam da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu sojoji.

Kafar labaran tsaro ta Zagazola Makama ta ruwaito cewa, wanda ake zargin da aka fi sani da Manci ya ba da bayanai ne ga ‘yan ta’addan a ranar 16 ga watan Maris kan motsin sojoji.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

Majiya ta bayyana cewa, bayanan sirri da Manci ya bayar ne ya kai ga yiwa sojoji kwanton bauna tare da tashin wasu daga cikinsu da bama-bamai IED.

Yadda dan Boko Haram ya ce ya tuba amma yake barna
Jihar Borno mai fama da Boko Haram | Hoto: channe;stv.com
Asali: UGC

Yadda aka samu mutuwar sojoji

Rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar TheCable na cewa, sojoji uku ne suka rasu, inda wasu hudu suka samu munanan raunuka a yankin Banki da ke jihar Borno.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar majiya, Manci na daga cikin 'yan ta’addan da suka mika wuya tare da ajiye makamai ga sojojin Najeriya, kuma ake yin hidimar sauya tunaninsu a sansanin gyaran hali.

Amma an zargi cewa, duk da mika wuya, Manci bai saduda ba, ya ci gaba da lika kansa ga kungiyar ta’addancin da kuma hada kai wajen aikata barna tare da tsoffin abokansa.

Manci bai bar barna da ta’addanci ba

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Daga kai kudin fansan a saki matarsa da 'ya'yansa, 'yan bindiga sun rike mai gida

Wasu majiyoyin tsaro sun naqalto cewa, a watan Faburairun da ya gabata nan ma Manci ya ba da bayanan sirri ga ‘yan Boko Haram, har ya kai ga an farmaki sojoji a garin Ngauri.

Bayanan sirri sun nuna cewa, wadannan kits-kitse da ya yi sun kai ga mutuwar sojoji da yawa a Najeriya.

Wannan lamari dai ya sake dasa ayar tambaya game da ci gaba da karbar tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram da ke barna a Najeriya.

A wani labarin, kunji yadda sojoji suka fatattaki ‘yan ta’adda a yanki Borni bayan da gwamnan jihar ya kada kuri’arsa a ranar zabrn gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel