Dakarun MNJTF Sun Kama Masu Taimakawa Yan Ta’adda 900 a Sambisa

Dakarun MNJTF Sun Kama Masu Taimakawa Yan Ta’adda 900 a Sambisa

  • Dakarun rundunar hadin gwiwa sun yi ram da wasu mutane fiye da 900 da ke da alaka da Boko Haram
  • MNJTF ta ce ana zargin mutanen da aka kama sun kasance iyalai da masu taimakawa mayalakn kungiyar ta'addanci ne
  • An kama su ne yayin wani aiki da sashi na uku da hudu na rundunar suka yi a yankin dajin Sambisa

Borno - Rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta ce dakarunta na sashi 3 da 4 sun yi nasarar kama iyalai da masu taimakawa mayakan Boko Haram su 900, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Babban jami'in hulda da jama'a na rundunar MNJTF da ke N’Djamena a kasar Chadi, Laftanar Kanal Kamarudeen Adegoke ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 15 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Kama Yan NNPP 2 Da Ke Shirin Tada Zaune Tsaye Yayin Zaben Gwamna a Kano

Dakarun rundunar sojojin Najeriya a motar yaki
Dakarun MNJTF Sun Kama Masu Taimakawa Yan Ta’adda 900 a Sambisa Hoto: Punch
Asali: UGC

Ya ce fadan cikin gidan da ake fama da shi tsakanin mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram da ISWAP, da kuma ruwan bama-baman da rundunar ke yi musamman ta sama sun taimaka sosai wajen hana mayakan zirga-zirga.

An kama mutanen a dajin Sambisa

Ya ce mutane masu dumbin yawa na ta zarya daga dajin Sambisa zuwa tafkin Chadi a cikin watan da ya gabata, rahoton Punch.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Laftanar Kanal Kamarudeen ya ce:

"A wani aiki na hadin gwiwa tsakanin rundunar MNJTF na sashi na 3 da 4 a da ke kogin Kamadougu Yobe, kan iyakar Najeriya da Nijar, an kama mutum fiye da 900 da suka hada da mata, yara da dattawa wadanda ake zaton iyalai da masu taimakawa yan ta'adda ne.
"Muna ci gaba da hada kai da hukumomin kasa da sannan ana tattara bayanai da mika wadannan mutane.

Kara karanta wannan

Dubu Wasu Yan Fashi Da Makami Sanye Da Kayan Sojoji Ya Cika, Sun Shiga Komadar Yan Sanda

"Har ila yau, dakarun sashi na 4 sun gudanar da fatrol din dare a hanyar Ngagam – Djalori inda suka ceto mata uku tare da yaransu hudu wadanda ke sterewa daga yaki tdakanin Boko Haram da ISWAP a dajin Sambisa.
"A wani lamari makamancin wannan, a ranar 8 ga watan Maris, dakarun sashi na 3 da aka tura Damasak, sun kama iyalana yan ta'adda 70 da suka hada da mata 43 da yara 30.
"Yanzu haka suna samun kulawar likitoci da kuma tattara bayanansu."

DSS ta kama masu shirin tada zaune tsaye a yayin zaben gwamnan Kano

A wani labarin, mun ji cewa rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta cika hannu da masu mambobin jam'iyyar NNPP biyu da ke shirin ta da zaune tsaye yayin zaben gwamna a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel