Rikici ya Barke Tsakanin Sojoji da ‘Yan Sanda, an Sheke ’Yan Sanda Biyu A Ofishin hukumar INEC

Rikici ya Barke Tsakanin Sojoji da ‘Yan Sanda, an Sheke ’Yan Sanda Biyu A Ofishin hukumar INEC

  • An samu hargitsi tsakanin 'yan sanda da sojoji a jihar Taraba yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna
  • Ya zuwa yanzu, an ce an hallaka jami'an 'yan sanda guda biyu, inda aka jikkata wasu jami'ai biyu nan take
  • Ya zuwa yanzu, hukumomin tsaro sun zauna domin tabbatar da an shawo kan lamarin da ya taso kwatsam

An hallaka jami’an ‘yan sanda biyu an kuma jikkata biyu yayin da fada ta barkewa tsakaninsu da sojoji a Jalingo da ke jihar Taraba a ranar Litinin.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa, an samu sabani ne tsakanin ‘yan sanda da sojoji a hedkwatar hukumar zabe ta INEC, lamarin da bai zo da dadi ba.

A cewar majiya, sojojin sun kori dukkan jami’an ‘yan sandan da ke bakin aiki ne a ofishin tattara sakamakon zaben jihar da ke hedkwatar INEC.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jama'a na ta kansu, ana ta harbe-harbe a kusa da' ofishin INEC a jihar Taraba

Yadda 'yan sanda biyu suka mutu a Taraba
Jihar Taraba, a Arewa maso Gabas | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

‘Yan sandan da suka samu rauni a halin yanzu an kai su asibitin tarayya da ke birnin Jalingo, kamar yadda majiyoyi daga jihar suka shaida, Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda barnar ta kasance, an lalata motoci

An ruwaito cewa, an lalata motocin da ke ajiye a cikin hedkwatar ta INEC a lokacin da rikicin ya yi kamari.

An kuma yi harbe-harbe da ya jawo tashin hankali ga mazauna yankin, har ta kai aka rufe shagunan da ke zagayen wurin, DailyPost ta tattaro.

A tattaunawa da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sulaiman Amodu ya ce, an shirya tawagar bincike mai zurfi don gano tushen lamarin.

Tattaunawar da kwamishinan ya jagoranta ta hada da kwamandan sojin Najeriya a Brigade 6 da ke Jalingo, Br. Janar Frank Etim da kuma daraktan hukumar DSS a jihar.

Kara karanta wannan

Buri ya cika: Daga cin zabe, sabon gwamnan Sokotomya fadi abubuwa 9 da zai yi

Yadda aka ji tashin rikici a Taraba

A baya kun ji yadda aka ruwaito cewa, an ji harbin bindiga daga wurare daban-daban kusa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kuma hedkwatar 'yan sanda.

Wannan lamari ya sa masu shaguna da sauran 'yan kasuwa tserewa suna rufe shagunansu don tsira da rayukansu.

An samu tashin hankali a lokacin da ake kokarin tattara sakamakon zaben jihar Taraa da ke Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel