Gobara Ta Sake Tashi A Wata Babban Kasuwar Borno, Hotuna Sun Fito

Gobara Ta Sake Tashi A Wata Babban Kasuwar Borno, Hotuna Sun Fito

  • An samu gobara a kasuwar Gamboru da ke unguwar Kwastam a Maiduguri a yau Asabar 18 ga watan Maris
  • Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne misalin karfe 3 na rana yayin da mutane ke kada kuri'arsu yayin zabukan gwamna da yan majalisun jiha
  • Babu cikakken bayani game da dalilin afkuwar gobarar wanda a halin yanzu amma dai jami'an kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar daga baya

Jihar Borno - Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru da ke kusa da unguwar Kwastam a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, rahoton Channels TV.

Kasuwar Gamboru ita ce kasuwa mafi girma na kayan gwari a Maiduguri.

Gobarar ta tashi ne misalin karfe 3 na rana kamar yadda HumAngle ta rahoto.

Gobara
Gobara Ta Sake Tashi A Wata Babban Kasuwar Borno, Hotuna Sun Fito. Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gobara a Borno
Gobara Ta Sake Tashi A Wata Babban Kasuwar Borno, Hotuna Sun Fito. Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Duk da cewa ba a san abin da ya yi sanadin gobarar ba a yanzu, Channels Television ta tattaro cewa akwai yiwuwar an tafka asarar kayayakin miliyoyin naira.

Mutane da suka kada kuri'a sun bar rumfunan zabe sun garzaya zuwa wurin da gobarar ke ci.

Kawo yanzu dai babu tabbas kan abin da ya yi sanadin gobarar, amma hakan na faruwa ne kimanin sati uku bayan babban kasuwa na birnin Maiduguri ya yi gobara.

Lamuran biyu sun faru yayin da mazauna jihar ke can suna kada kuri'a don zaben sabbin shugabanni.

Gobarar ta kasuwar Gamboru shima ya faru ne awanni kadan bayan wani gobarar ta faru a garin Biu da ke kudancin Borno, inda wuta ta cinye wani sashi na masu sayar da katako.

HumAngle ta ziyarci wurin da gobarar ta faru kuma ta lura yadda yan kasuwan ke kallon gobarar a yayin da jami'an kashe gobara ke kokarin shawo kan abin.

An Yi Gobara A Babbar Kasuwar Maiduguri A Jihar Borno

A wani rahoto a baya kun ci cewa an yi gobara a babban kasuwar 'Monday Market' a Borno.

A cewar rahoton gobarar ta fara ne misalin karfe 2.00 na dare a ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairu, sannan ta bazu zuwa wasu bangarori a kasuwar.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, gobarar ta lalata shaguna masu yawa sosai kuma an tafka asarar miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel