Jerin Gwamnonin Najeriya da Ka Iya Rasa Damar Yin Tazarce Zuwa Wa’adi Na Biyu, Da Dalilai

Jerin Gwamnonin Najeriya da Ka Iya Rasa Damar Yin Tazarce Zuwa Wa’adi Na Biyu, Da Dalilai

Akalla gwamnoni 11 ne ke neman tazarce a zaben gwamnoni da za a yi a Najeriya a ranar 18 ga watan Maris da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa.

Sai dai, wane irin kalubale ne a gaban wasu daga cikinsu? meye ake hasasowa game da nasararsu a zaben? Kana yaya tasiri da yiwuwar nasararsu za ta kasance.

A wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta tattaro jerin wasu gwamnoni 5 da ke neman wa’adi na biyu a mulki, amma kuma ta yiwu su ci taliyar karshe.

Tasgaron da wasu gwamnoni ka iya samu
Na'urar tantance masu kada kuri'u a Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

1. Gwamna Sanwo Olu na Legas

Gwamna Sanwo Olu na jihar Legas na daga cikin gwamnonin da ke da tasiri a Najeriya, musamman yadda ake ji da Legas a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Abba Kabir-Yusuf: Dan Takarar Gwamnan NNPP Da Ya Kwace Kano Daga Hannun APC

Sai dai, akwai yiwuwar gwamnan ya ci taliyar karshe, duba da yadda sakamakon zaben shugaban kasa ya kasance a Najeriya.

A zaben da ya gabata na shugaban kasa, dan takarar shugaban kasa na Labour ne ya lashe zabe a Legas, duk da kuwa Bola Tinubu na APC dan asalin jihar ta Legas ne.

A bangaren APC, Tinubu ne kusan mu’assasinta, kuma ya yi mulki a Legas na tsawon shekaru 8 baya ga kasancewarsa sanata, haka nan matarsa, amma duk da haka bai ci Legas ba.

A hasashe, wannan ka iya zamewa Sanwo Olu babban kalubale a zaben gwamnan jihar, ganin yadda Labour ta karbu, ga kuma dan takarar PDP Jandor ya kunno kai.

2. Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa

A wani yanayi mai kama da taron dangi, jam’iyyun siyasa da yawa, ciki har da Labour sun hada kai da APC don tabbatar da tumbuke Ahmadu Fintiri.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

Alamu masu karfi na nuni da cewa, Fintiri zai iya samun tasgaro daga Aisha Binani, ‘yar takarar APC da ke da goyon bayan shugabannin APC mai ci a kasar da kuma uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari.

Kasancewarsa mai goyon bayan Atiku, Fintiri na ci gaba da fuskantar barazana daga jam’iyyar adawa, ga kuma Atiku na PDP, dan asalin jihar Adamawa bai lashe zaben shugaban kasa ba.

Faduwar Atiku da kuma tasirin Aisha Binani na iya zama tasgaro ga Fintiri a zaben na gwamnoni da ke tafe nan kusa.

3. Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe

A bangare guda, gwamna Inuwa Yahaya na iya fuskantar kalubale a zaben bana, duk da kuwa gwamnan ya yi aiki tukuru a jiharsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kasancewar jam’iyyar PDP ce ta fi samun kuri’u a jihar Gombe a zaben da ya gudana na shugaban kasa, Inuwa Yahaya ka iya fuskantar matsala a zaben gwamnoni.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zaben Gwamna: APC Ta Yi Gagarumin Gargadi Ga Al'ummar Wata Jihar Kudu

‘Yan takarar PDP da NNPP na iya ba da mamaki a zaben, duba da yadda suka samu karbuwa a idon ‘yan jihar idan aka yi la’akari da zaben shugaban kasa.

4. Gwamna Bala Muhammad na Bauchi

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ka iya samun tsaiko a zaben bana, wanda hakan babban barazana ne ga yin tazarcensa.

Akwai tasiri mai karfi na jam’iyya mai mulkin kasa ga zabuka, don haka zai iya fuskantar karfin iko.

Bugu da kari, dan takarar APC, AM Sadeeq Abubakar ya kasance tsohon hafsun sojin sama, ambasadan Najeriya, kuma mijin minista, Sadiya Umar Faruk.

Alamu na nuna cewa, mijin minista na ciya ciyar da Bala taliyar karshe idan har lamura suka cabe masa.

5. Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa

A bangare guda, gwamnan Nasarawa na iya fuskantar kalubale a zaben gwamnoni idam aka yi la’akari da sakamakon zaben shugaban kasa.

A zaben da ya gabata, Peter Obi ne ya fi kowa tattara kuri’u a jihar Nasarawa, lamarin da ka iya shafar zaben gwamna na 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Sa An Gaza Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Hakazalika, jam’iyyun AA, SDP, PRP da NNPP sun gama kai don ganin sun tabbatar da tsige gwamnan mai ci na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel