Zaben 2023: Kotu Ta Bada Sabuwar Hukunci A Karar Da PDP Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

Zaben 2023: Kotu Ta Bada Sabuwar Hukunci A Karar Da PDP Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima

  • Kotun daukaka kara ta bada sabon hukunci a karar da jam'iyyar PDP ta shigar kan Bola Tinubu da Kashim Shettima na jam'iyyar All Progressives Congress, APC
  • Kotun, a sabon hukuncin, ta yanke hukunci cewa karar ba ta da nagarta na kallubalantar zabin yan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress APC a zaben da aka kammala
  • PDP ta kallubalanci halascin tikitin Tinubu/Shettima, tana mai cewa zaben Shettima ya saba tanade-tanaden sashi na 29(1), 33, 35, da 84 (1) (2) na dokar zaben 2022

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara na Abuja ta jingine zartar da hukunci kan karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta shigar na neman soke zaben Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki a na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Kara karanta wannan

Ba mu yarda ba: Yarbawa sun ce Tinubu bai ci zabe ba, sun fadi wanda ya lashe zaben bana

A daukaka karar, PDP ne neman a jingine hukuncin ranar 13 ga watan Janairu da Mai shari'a Inyang Ekwo na babban kotun Abuja ya yi.

Tinubu da Shettima
Kotu ta yi watsi da karar kallubalantar zabin Tinubu da Shettima. Hoto: Photo credit: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta jingine yanke hukunci

Alkalin ya yi watsi da karar saboda jam'iyyar ta PDP ba ta da hurumin a karkashin doka na yin katsalandan kan yadda APC ke zaben yan takarar ta, jaridar The Sun ta rahoto.

Kwamitin mambobin wata uku a kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani, bayan nazarin batutuwan da bangarorin biyu suka gabatar, sun ce sun jingine zartar da hukunci zuwa wani rana a gaba, da za a sanar da bangarorin biyu.

Atiku ya tafi gidan IBB a Minna, sun yi ganawar sirri

A wani rahoto, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya kai wa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidansa da ke Minna.

Kara karanta wannan

PDP Ta Kori Sanata Nnamani Mai Yi Wa Tinubu Kamfe, Ta Kwace Tikitin Takararsa

Wazirin Adamawan ya isa filin tashi da saukan jirage na Minna da karfe 11 na safiya kuma Dr Mu'azu Babangida Aliyu, tsohon gwamnan Neja da wasu manyan mutane suka tarbe shi.

Rahotanni sun ce ziyarar da Atikun ya kai ba za ta rasa nasaba a sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar INEC ta fitar ba a baya-bayan nan da wasu jam'iyyun hamayya suka yi watsi da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel