Atiku Abubakar Ya Yi Ganawar Sirri Da IBB A Gidansa Da Ke Minna

Atiku Abubakar Ya Yi Ganawar Sirri Da IBB A Gidansa Da Ke Minna

  • Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023 ya ziyarci Ibrahim Badamasi Babangida a Minna, Jihar Neja
  • Ziyarar ta Atiku ba za ta rasa nasaba da zaben shugaban kasa da aka yi a baya-bayan nan ba da ya ke kallubalantar sakamakon a kotu
  • Hakazalika, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ziyarci IBB don masa maraba bayan dawowarsa daga kasar waje don magani

Minna - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar a ranar Laraba ya ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya dira a filin sauka da tashi jirage na Minna misalin karfe 11 na safe kuma tsohon gwamnan Minna, Dr Mu'azu Babangida Aliyu ya tarbe shi.

Kara karanta wannan

DSS Ta Kama Mambobin Jam'iyyar PDP 3 A Kaduna 'Kan Shirin Tada Rikici' Yayin Zaben Gwamna Da Majalisun Jiha

Atiku
Ma'uazu Babangida Aliyu, tsohon gwamnan Neja da baki sun tari Atiku a Minna. Hoto: Channels TV.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga nan kuma ya tafi gidan dattijon kasar da ke Minna kamar yadda The Channels ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa sun yi taro na fiye da awa guda.

Dalilin ganawar Atiku da IBB a Minna

A cewar bayanai ziyarar ba ta rasa nasaba da zaben da aka kammala a kasar da kuma yin korafi a hukumance kan yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kasa gudanar da sahihin zabe mai inganci da karbuwa tare da kin amincewa sakamako da soke zaben.

Kuma, Atiku Abubakar ya isa Minna don maraba da Janar Babangida bayan dawowarsa daga kasar waje inda ya tafi duba lafiyarsa.

Atiku ya sha kaye hannun babban abokin hamayarsa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu wanda ya samu kuri'u 8,794,794. Ya zo na farko a jihohi 12 na Najeriya cikin 36 kuma ya samu isasun kuri'u a wasu jihohin tare da samun kuri'u mafi rinjaye baki daya.

Kara karanta wannan

“Ku Sarara Mun, Ku Ma Kun Fadi Zaben Sanata”: Atiku Ya Yi Wa Gwamnonin G5 Da Wike Ke Jagoranta Wanki Babban Bargo

Tsohon mataimakin shugaban kasar dan shekara 76, wanda yanzu ya yi takarar shugaban kasa sau shida, ya samu kuri'u 6,984,520 yayin da dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi, ya samu kuri'u 6,101,533 inda ya zo na uku.

Atiku da Obi duk ba su gamsu da sakamakon zaben ba kuma sun garzaya kotu don kallubalantar sakamakon zaben.

Za mu kwace jihar Nasarawa daga hannun APC, In Ji SDP

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar SDP a jihar Nasarawa, ya ce yana da tabbas cewa jam'iyyarsa za ta kwace jihar daga hannun gwamnatin APC.

Muhammad Mustapha ya furta hakan ne a wani hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel