Kungiyar Yarbawa Ta Afenifere Ta Ce Bata Amince da Nasarar Tinubu Ba, Ta Ce Peter Obi Ne Ya Ci Zabe

Kungiyar Yarbawa Ta Afenifere Ta Ce Bata Amince da Nasarar Tinubu Ba, Ta Ce Peter Obi Ne Ya Ci Zabe

  • Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana dan takarar da ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu a ra'ayinta
  • A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar, Peter Obi ne a zahirance ya lashe zaben ba wai Bola Ahmad Tinubu ba
  • Sun kuma barranta da dansu Bayarbe, Bola Ahmad Tinubu da INEC ta ce shine ya lallasa Obi da Atiku a zaben bana

Jihar Ogun - Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta tsaya tsayin daka cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ne ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu.

A cewar kungiyar, sam ba Bola Ahmad Tinubu bane ya ci zaben da aka kammala a makwanni biyu da suka gabata ba.

A ranar Talata 7 ga watan Maris, Afenifere ta ce, Peter Obi ya yi daidai da ya dauko batun kai kara kotu don tabbatar da karbar hakkinsa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta ba Tinubu damar yin kwafin takardun da INEC ta yi aiki dasu a zaben shugaban kasa

Bola Ahmad Tinubu bai ci zabe ba, inji Afenifere
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Yarbawa sun yi zama, sun ce Obi ne ya ci zabe

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan ganawa tsakanin shugabanninta a Isanya-Ogbo a jihar Ogun ranar Talata, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kungiyar ta ce ta yi Allah-wadai da duk wani batu da ake alakanta ta dashi kan nasarar Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC.

Idan baku manta ba, Atiku da Obi sun garzaya kotu domin kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa na bana.

An ba Obi da Atiku damar bincika takardun aikin zabe

A bangare guda, kotun daukaka kara ya ce ya ba Atiku da Obi damar bincika takardun da INEC ta yi amfani dasu a aikin zaben na shugaban kasa na bana.

Wannan na zuwa ne yayin da Obi da Atiku suka bukaci samun takardun don duba inda aka samu matsala don su samu damar titsiye Tinubu a kotu.

Kara karanta wannan

Afenifere Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Bayyana Dan Takarar Da Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Daga nan ne kotun yace, Atiku da Obi za su iya bincike, yin kwafin takardu da sauran kayayyakin aikin zabe masu muhimmanci ba tare da wata matsala ba.

A bangaren APC, an ba Bola Ahmad Tinubu irin wannan dama don ya samu damar kare kansa daga titsiyen ‘yan adawa a gaban kotu game zaben da aka gudanar.

Kotun daukaka karan ya ce, Tinubu ma na da damar samun kwafin takardun tare da bincike duk abin da yake so a ciki ba tare da wata tsangwama ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel