Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Katsina a NNPP Ya Marawa Dan Takarar Gwamnan APC Baya

Dan Takarar Mataimakin Gwamnan Katsina a NNPP Ya Marawa Dan Takarar Gwamnan APC Baya

  • Abokin takarar Nura Khalil, dan takarar gwamna a jihar Katsina ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan jam’iyyar APC
  • Rabe Darma ya ce Katsinawa na bukatar mutum mai hali irin na Dikko Radda don ciyar da jihar gaba mai dorewa bayan zaben 2023
  • Ana ci gaba da shirin zaben 2023 na gwamnoni, ‘yan siyasa na musayar magoya baya gabanin zaben da ke tafe nan kwanaki takwas

Jihar Katsina - Rabe Darma, abokin takarar Nura Khalil mai hango kujerar gwamna a Katsina karkashin jam’iyyar NNPP ya bayyana goyon bayansa ga Dikko Radda, dan takarar gwamnan APC a jihar.

Darma ya bayyana yana tare da dan takarar na APC ne a ranar Alhamis 9 ga watan Maris a jihar ta Katsina, rahoton jaridar TheCable.

Ya shaida cewa, idan Radda ya samu nasara a zaben na bana, tabbas zai kawo ci gaba a jihar mai dorewa kuma wanda ake bukata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi: Duk da Yana PDP, Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Ayyana Goyon Baya Ga Dan Takarar APC

Darma ya koma tsagin Radda a Katsina
Lokacin da Rabe Darma ya gana da Dikko Radda | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Katsina na bukatar mutum irin Radda, inji Darma

Darma ya ce, jihar na bukatar mutum mai nagarta irin ta Radda; mai gaskiya da amana don ciyar da ita gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Dr Dikko Radda na da abin da ake bukata da gogewar da zai fitar da jihar daga kungurmin halin da take ciki; muna bukatar cimma manufofinsu.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar NNPP mai kayan marmari da su goyi bayan dan takarar gwamnan APC a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.

Radda ya yi martani, Khalil ya ce an ci amanarsa

Da yake murna da alherin Darma, Radda ya yaba masa bisa bashi goyon baya, kuma ya yi alkawarin damawa dashi idan ya hau karagar mulki, rahoton Vanguard.

A nasa bangare, dan takarar gwamnan NNPP Khalil ya ce abin da abokin takarar tasa ya yi ba komai bane face tsagwaron cin amana.

Kara karanta wannan

Fada Ya Kaure Tsakanin Yan Daban APC da PDP, An Yi Kisa a Jihar Arewa, Da Dama Sun Jikkata

Ya bayyana cewa:

“Ban san da wata alaka ba. Wannan abu ba zai karya min gwiwa ba daga kokarina na ganin na zama gwamnan jihar Katsina.
“Abin kunya ne yadda abokin takara ta kuma jigon NNPP ya so siyar da jam’iyya.”

Alamu sun nuna Radda na ci gaba da samun nasara da karbuwa a Katsina, a makon da ya gabata ne jiga-jigan PDP suka sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel