Da Walakin: Bayan Rikicinsa Da 'Yan APC, Dogara Ya Marawa Dan Takarar Jam'iyyar Baya a Zaben Gwamnan Bauchi

Da Walakin: Bayan Rikicinsa Da 'Yan APC, Dogara Ya Marawa Dan Takarar Jam'iyyar Baya a Zaben Gwamnan Bauchi

  • Yakubu Dogara ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar APC, Air Marshall Sadiq Baba Abubakar, a jihar Bauchi
  • Tsohon kakakin majalisar wakilai ya bukaci al'ummar jihar Bauchi da su fatattaki Sanata Bala Mohammed daga mulki
  • Hakan na zuwa ne yan kwanaki kafin zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris

Bauchi - Tsohon kakakin majalisar wakilai, Hon. Yakubu Dogara, ya ayyana goyon bayansa ga Air Marshal Sadiqque Baba Abubakar mai ritaya, dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi.

Kwanaki Dogara ya yi suka tare da nuna adawa da tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa, yana mai cewa kamata yayi ace jam'iyyar ta samu Kirista daga arewa.

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara
“Akwai Bukatar a Sauya Bala Mohammed”: Dogara Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Dan Takarar Gwamnan APC a Bauchi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Hakazalika ya koma bayan Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Fada Ya Kaure Tsakanin Yan Daban APC da PDP, An Yi Kisa a Jihar Arewa, Da Dama Sun Jikkata

A halin da ake ciki, tsohon kakakin majalisar wakilan ya jagoranci wata tawaga ta Air Marshal Abubakar mai ritaya a fadin wasu kananan hukumomi ciki harda Kirfi da Alkaleri inda gwamna mai ci Bala Mohammed ya fito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga dandazon magoya baya a karamar hukumar Alkaleri ta jihar, Dogara ya bukaci mutanen da su fatattaki Bala Mohammed daga kujerar shugabanci a ranar 18 ga watan Maris, rahoton Leadership.

Dogara ya ce:

"Mun zo mu fada maku gaskiya, cewa akwai bukatar chanjin shugaba a jihar Bauchi. Na zo nan don wayar maku da kai cewa koda dai danku (Gwamna Bala Mohammed) yana wajen amma tunda baya kokari, mu sauya shi. Ina mai umurtanku da ku kada kuri'unku ga Air Marshal Sadiqque Abubakar a ranar Asabar."

Ya bayyana Air Marshal Abubakar a matsayin uba wanda zai kawo ci gaba ga mutanen jihar Bauchi, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta ba Tinubu damar yin kwafin takardun da INEC ta yi aiki dasu a zaben shugaban kasa

Ku tuna cewa alaka ta yi tsami tsakanin Dogara da Bala Mohammed bayan ya zarge shi da take yarjejeniyar da suka shiga kafin zaben 2019, wanda ya kawo gwamnan karagar mulki.

An yi kazamin karo tsakanin yan daban APC da PDP a Bauchi

A wani labari, mun ji cewa rikici ya kaure tsakanin yan daban APC da PDP a jihar Bauchi wanda ya yi sanadiyar salwantar rai guda da kuma jikkata wasu da dama.

Lamarin ya afku ne lokacin da dan takarar gwamnan PDP ya ziyarci mahaifar Gwamna Bala Mohammed na PDP wato Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri don yin kamfen.

Rahotanni sun kawo cewa a nan ne rikici ya barke lamarin da ya kai ga har an yi musayar wuta a tsakani.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel