“Ba Zan Sake Aure Ba a Rayuwata”: Yar Najeriya Ta Koka, Ta Yi Danasanin Aurenta

“Ba Zan Sake Aure Ba a Rayuwata”: Yar Najeriya Ta Koka, Ta Yi Danasanin Aurenta

  • Wata matashiya ta sa mutane tofa albarkacin bakunansu a soshiyal midiya bayan ta koka kan kalubalen da take fuskanta a gidan aurenta
  • Matashiyar mai suna Bella ta sharbi kuka da hawaye yayin da take nuna bakin ciki cewa bata san haka aure yake ba
  • Bella ta sha alwashin cewa ba za ta sake aure ba a rayuwarta, lamarin da ya jefa mutane cikin halin kaduwa

Cike da hawaye, wata matar aure mai suna Bella ta fadama jama'a cewa abubuwa basa tafiya daidai a gidan aurenta.

Matashiyar ta yi wata wallafa a shafin TikTok inda aka gano ta cikin hawaye shame-shame dauke da taken, " Ba zan sake aure ba a rayuwata."

Matashiya tana sharban kuka da hawaye
“Ba Zan Sake Aure Ba a Rayuwata”: Yar Najeriya Ta Koka, Ta Yi Danasanin Aurenta Hoto: @bellakiss022
Asali: TikTok

Bella ta ce bata taba tsammanin rayuwar aurenta zai shiga halin da yake ciki a yanzu ba. Sai dai kuma bata fito fili ta bayyana menene matsalar da take fuskanta ba.

Kara karanta wannan

Shirin Ya Kwance: Amarya Ta Karye Ana Saura Kwana Kaɗan Biki, Ta Je Wajen Biki a Keken Guragu

Wallafar tata ya yi fice a manhajar ta TikTok, inda mutane da dama ke kokarin karfafa mata gwiwa inda suka kawo mata misalai da rayuwar aurensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu na mamakin me ya sa har ta shiga wannan yanayi mai tsuma zuciya.

Kalli wallafarta a nan:

Jama'a sun yi martani

GIFTED ta ce:

"Dan Allah kada ki tsorata ni nawa auren zai tafi daidai kamar yadda littafd=i mai tsarki ya ce...ki yarda ko kada ki yarda, na bude shafin murna a rayuwata."

Nurs Munachi Charles ta ce:

"Ban san labarinki ba, amma magana ta gaskiya, shekaru biyar na farko a rayuwar aure na da matukar wahaka saboda har lokacin kuna kokarin fahimtar juna."

lady ta ce:

"Haka nima a nan fahh ba zan yi aure ba.
"Uban dana ya gasa mun aya a hannu.
"Idanuna basa taba bushewa da hawayen kunar rai."

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Mai Kula Da Fasinjojin Jirgin Sama Ta Ɗauki Juna Biyu Ba Ta Sani Ba, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Villageharrypotter ya ce:

"Hehehehe na yarda dake??? matar aure da hujin hanci? Woh ba sai na ji labarinki bake ce da laifi."

TemmyAkins ta ce:

"Aure na da dadi idan kika hadu da nagari amma bincikena ya sa na fahimci cewa idan kika hadu da miji nagari, za ki fuskanci jarrabawa."

Jarumin Kannywood, Tijjani Asase ya sake shiga daga ciki a karo na biyu

A wani labari na daban, mun ji cewa fitaccen jarumin Kannywood, Tijjani Asase ya angwance da kyakkyawar amaryarsa a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel