Ana Saura Sati Ɗaya Biki, Amarya Ta Karye Ta Ɓishe Da Zuwa Waajen Bikin a Keken Guragu

Ana Saura Sati Ɗaya Biki, Amarya Ta Karye Ta Ɓishe Da Zuwa Waajen Bikin a Keken Guragu

  • Wata budurwa ƴar Najeriya wacce akai aurenta tana kan keken guragu ta sha yabo sosai a yanar gizo
  • Budurwar wacce ke da aukin jiki ta faɗi wanda a sanadiyyar hakan ƙafarta ta karya ana sauran sati ɗaya bikin ta.
  • Duk da wannan koma baya da ta samu, budurwar ta samu ta halarci bikin nata cikin wata shiga wacce ta ƙayatar

Wata budurwa ƴar Najeriya ta ƙare da yin aure akan keken guragu bayan ta faɗi ta samu karaya a ƙafarta.

Wata ta kusa da amaryar sabon aure wacce ta sanya bidiyon bikinta a TikTok, ta bayyana cewa budurwar faɗi ne ana sauran kwana bakwai bikin ta.

Miji da mata
Ana Saura Sati Ɗaya Biki, Amarya Ta Karye Ta Ɓishe Da Zuwa Waajen Bikin a Keken Guragu Hoto: TikTok/mhizcherish20
Asali: UGC

Ta bayyana cewa shaiɗan ya makaro inda ta miƙa godiyar ta ga ubangiji bisa yadda akai bikin cikin nasara duk kuwa da koma bayan da amaryar ta samu.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Mai Kula Da Fasinjojin Jirgin Sama Ta Ɗauki Juna Biyu Ba Ta Sani Ba, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Ta sanya bidiyon yadda aka gudanar da bikin a cikin coci inda take cewa, nufin ubangiji ne yiwuwar auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama a yanar gizo sun yabawa jarumtar amaryar da mijinta inda suka nuna godiyar su ga ubangiji bisa nasarar da ya bayar tayin auren masoyan biyu.

Ga kaɗan daga ciki:

EVERYTHING LOLU ta rubuta:

"Wannan cikakken namiji ne, kai akwai daɗi namiji ya so ka fiye da yadda kake son shi oo."

dallahs ta rubuta:

"Ƴar'uwata, tabbas shaiɗan ya makara. Zai cigaba da makara a koda yaushe."

jummy ta rubuta:

"Wannan cikakken namiji ne ooo. Ina taya ku murna, na ji muku daɗi sosai, ubangiji ya albarkaci auren ku."

Olahipsy ya rubuta:

"Karaya a ƙafa tana da matuƙar wahala"

tiwa la porch ta rubuta:

"Ina taya ku murna, na ji muku daɗi sosai, nima ina addu'ar ubangiji ya bani muradin zuciya ta."

Kara karanta wannan

"Ina Cikin Tsaka Mai Wuya Mijina Ya Matsa Sai Na Ba Mahaifiyarsa Mara Lafiya Ƙoda Ta", Matar Aure

Bidiyon Ango Na Sharɓar Kuka a Wajen Ɗaurin Auren Sa Ya Ɗauki Hankula

A wani labarin na daban kuma, wani ango ya zo da sabon salo a ranar ɗaurin auren sa, kan wani abu da yayi.

Angon dai gwanin ban mamaki ya saki baki kamar wani ƙaramin yaro yana ta sharɓar kuka lokacin da ya hango amaryar sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel