Jarumin Kannywood, Tijjani Asase, Ya Angwance Da Santaleliyar Budurwarsa

Jarumin Kannywood, Tijjani Asase, Ya Angwance Da Santaleliyar Budurwarsa

  • Jarumin fim Tijjani Abdullahi Asase ya angwance da zukekiyar amaryarsa mai suna Khadija
  • Tuni hadaddun hotunan shagulgulan bikin suka karade soshiyal midiya inda amarya da ango suka fito shar da su
  • Mabiya shafinsa na soshiyal midiya sun yi masa fatan alkhairi da addu'an zaman lafiya a gidan aurensu

Shahararren jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Tijjani Abdullahi wanda aka fi sani da Asase ya kara aure.

Tijjani Asase wanda ya fi fitowa a matsayin dan daba ya ankwance da kyakkyawar budurwarsa Khadija Ɗahiru Mu’azu Kyalli a karshen makon jiya.

Jarumi Tijjani Asase da amaryarsa a wajen dina
Jarumin Kannywood, Tijjani Asase Ya Angwance Da Santaleliyar Budurwarsa Hoto: Tijjani Asase
Asali: Instagram

Kamar yadda Fim Magazine ta wallafa, an daura aurensu ne a ranar Asabar, 4 ga watan Maris, da karfe 11:00 na safe a jihar Kano.

An dauki tsawon kwanaki uku ana gudanar da shagulgulan bikin kama daga majalisin yabon Annabi, zuwa ga saukar karatun Al-Kur'ani mai girma.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari da Tsohon Gwamna Su na Hangen Shugabancin Majalisar Dattawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, an yi ranar Larabawa a ranr Alhamis kafin daga karshe aka rufe da kasaitaccen bikin dina wanda aka yi wajen taro na Ali Jita Events Centre da ke garin Kano.

Amarya Khadija ita ce matar Asase ta uku, domin dai uwargidarsa ta rasu daga bisani ya sake aure inda ya kara a yanzu dai matansa biyu.

Jarumin ya wallafa hotunan shagalin bikin nasa a shafinsa na Instagram yana mai godiya ga yan uwa da abokan arziki da suka taya shi raya wannan rana.

Ya wallafa a shafinsa:

"Allah Nagode Maka Allah ya sakamuku da alkairin Amin."

Jama'a sun taya shi murna

mudassirhaladu_barkeke:

"Allah yasanya Alkhairi yabada zama fly da zuri'a Dayyiba @tijjaniasase_real"

mall.a9304:

"Allah yabaku zaman lfy da zuriya daiyiba Amin ya Allah."

abubakarjumcy

"Allah yabada zaman lafiya da Xuri'a dayyiba."

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

official_ibrahim_kanu04:

"Allah Sanya Alkhairi"

realkgaladimamuhd:

"Allah Ya Sanya Alkhairi Ya bada Zaman Lafiya da Zuri'a Dayyiba"

abbabeenadam:

"Allah ya sanya alkhairi❤️❤️."

imrana5627:

"Masha Allah Fatan alkhairi gareku Allah ya Kara Lpy da zaman lapiya ya sanya alkhairi"

abdoulrazak.bello.37:

"Allah ya bada zaman lfy alfarma annabi Mahamadou s à w ❤️❤️"

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu a soshiyal midiya bayan ganin bidiyon wani leshi da aka tallata kan miliyan N4.5 kowani yadi 5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel