Yanzu-Yanzu: Ba'a Zubda Gari A Ɗebe Duka Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Yanzu-Yanzu: Ba'a Zubda Gari A Ɗebe Duka Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

  • Dan Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC Yasha Kayi A Jihar Da Yafi Karfi ga Obi.
  • Tinubu Yace, Daman ita Rayuwa Haka take, Bazaka Samu Komai ba, Dole Ka Samu Wani Abu Ka Rasa Wani.
  • Bola Ahmed Tinubu Wanda ake Ma Kirari da "City Boy" Ya hori Mutanen Lagos da Su Zauna Lafiya Kada Sakamakon Ya Tunzura su.

Lagos - Ƴan siyasa sun yarda a koda yaushe su faɗi a ko ina, amma banda tsakar gidan su, wato wajen da suka fito.

Faɗuwa ga ƴan siyasa a cikin gida a mafi akasarin lokuta wata alama ce dake nuna rashin tasiri da rashin aikata abin azo a gani ga mutanen gida, yanki ko sashe.

Kamar yadda aka sani, ɗan takarar jam'iyyar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC, wato Bola Ahmed Tinubu bai samu nasarar kawo jihar sa ta Legos ba.

Kara karanta wannan

Mun gano INEC Na Ƙirƙirar Ƙuri'un Shafcin Gizo-da-Koƙi - Shugaban Labor Party

Tinubu
Ba'a Zubda Gari A Ɗebe Duka Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos. Hoto: Legit.ng
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da cewa Tsohon gwamnan ana ganin shine mutumin daya saita Legos alan cigaban da take tunƙaho dashi a yanzu tare da kafa jigajigan yan siyasa da suke riƙe da madafun iko a lungu da saƙo na ƙasar nan.

To sai dai Bola Ahmed Tinubu ya magantu akan wannan maganar, inda yace wannan faɗuwa da yayi a gida, ko a jikin sa.

Tunda fari dai, Peter Obi n Labor Party kwamishinan zaɓen jihar Legas ya ayyana a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a Legas, yanki mafi ƙarfi da Tinubu yake tunƙaho dashi.

Jim kaɗan da ayyana Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaɓen na jihar Legas, Tinubu yace sakamakon zaɓen bazai zama wani dalili na tunzura mutane ba.

Jaridar The Cable ta ruwaito Tinubu yana faɗin:

Kara karanta wannan

Yanzu: Jam'iyyar Labor Party Tayi Kira Da Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa

"Saboda APC tayi rashin nasara akan wata jam'iyya a Legas, ba dalili bane dazai sa adin ga rikici ba. Domin ita rayuwa, haka take, kayi nasara yau nan gobe ka rasa acan.
"Hasali ma, ba'a Zubda Gari a ɗebe duka. Saboda haka, dole ne mu ƙyale gudanar da zaɓen da tattara sakamako ya cigaba da gudana cikin salama," Inji shi.

Bola Tinubu, ya ƙarƙare da horon mabiya bayan sa da gujewa tsokana da kuma tashin tashina saboda wannan rashin nasarar da yayi ga Peter Obi har gida.

Yan Sanda Sun Cafke Lakcara Ɗauke Da Na'urorin Tantance Masu Kaɗa Ƙuri'a

Ƴan sanda sun yi babban kamu, inda suka cafke wani matashi ɗauke da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a a jihar Cross Rivers.

Wannan matashin mai katoɓara yayi sojan gona ga jami'in tattara sakamakon zaɓe na hukumar zaɓe ta INEC a jihar Cross Rivers, domin aikata ba daidai ba.

Amma tuni tuni jami'an hukumar ƴan sanda suka tasa ƙeyar sa domin cigaba da samun muhimman bayanai daga wajen sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel