Mun gano INEC Na Ƙirƙirar Ƙuri'un Shafcin Gizo-da-Koƙi - Shugaban Labor Party

Mun gano INEC Na Ƙirƙirar Ƙuri'un Shafcin Gizo-da-Koƙi - Shugaban Labor Party

  • INEC na Haɗa Sakamakon Ƙanzon Kurege Tana Yaɗawa a Matsayin Na Gaske.
  • Ba Zamu Amshi Duk Wani Sakamakon da Ba'a Rumfar Zaɓe aka Samo Ba Ko Wani Irine
  • Jam'iyyar ta nanata Cewa Indai Za'ai Zaɓe na Gaskiya Itace da Nasara Babu Haufi

Zaɓen shugaban ƙasa yazo ya tafi yabar baya da ƙura, musamman ga jam'iyyun dake shan kayi tare da ɗiban duka irin na karen mahaukaciyar birni.

Daga bangaren zaben yan majalisu ma abin ba'a cewa komai, domin kuwa jam'iyyu da dama ne suka bayyana rashin jin daɗin yadda sakamakon yake zuwan musu.

Ga wasu jam'iyyun sun samu sakamakon zaɓen ne a hannun hagu, watakila shi yasa suke ta zayyana ɓacin ran su da kuma tsarin matakin da zasu ɗauka nan gaba.

labour
Mun gano INEC Na Ƙirƙirar Ƙuri'un Shafcin Gizo-da-Koƙi - Shugaban Labor Party hoto: Labourpart.com.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yanzu: Jam'iyyar Labor Party Tayi Kira Da Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa

Itama jam'iyyar Labor Party Ba'a Barta a Baya ba, a salon nuna irin wannan korafi.

Domin tuni jam'iyyar tabi sahun jam'iyyu masu ganin zaɓen bai masu kyau, inda sukai ƙorafi da yin maguɗi tare da ƙirƙirar sakamakon da babu shi daga ɓangaren INEC.

Jihohin da jam'iyyar ta Labour Party tayi ƙorafi akai sun haɗa da jam'iyyar Lagos, Edo, Rivers da kuma Imo.

A wani taron manema labarai da jam'iyyar ta kira a Abuja. Shugaban jam'iyyar Julius Abure yayi martani akan wannan balahira cike da jimami akan yadda aka dinga musgunawa magoya bayan su.

Jam'iyyar tayi amfani da wannan damar wajen kira ga hukumar zaɓe ta ƙasa da a gaggauta soke zaɓen shugaban ƙasa gabaki ɗayan sa.

Jam'iyyar tace sakamakon da ake kawowa daga sauran sassan kasar ba wani abu face shafcin gizo da ƙoƙi, musamman ma zaɓen Rivers.

Jam'iyyar ta Labor Party ta roƙi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daya cika alƙawarin daya dauka na ganin an gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Ina da Tabbacin Tinubu da Sauran Ƴan APC ne Zasuyi Nasara Tun a Zagayen Farko - Buhari

Daga ƙarshe sun ƙarƙare da cewar, ba zasu amshi duk wani sakamako ba idan ba sahihi bane da aka samo a rumfunan kaɗa kuri'a ba.

A wani ɓangaren kuma an ruwaito yadda wani ɗan majalisar jihar kogi ya riga mu gidan gaskiya. Ko tayaya hakan ta faru?

Alhini Abin Da Yasa Dan Majalisar Jihar Kogi Ya Rasu Bayan Zabe

A cewar wani rahoton da The Punch ta wallafa, Omiata ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu a wani asibiti da ke Legas inda ya ke jinyar wata rashin lafiya da ba a bayyana ba

Femi Olugbemi wanda shine babban sakataren watsa labarai na majalisar jihar Kogi, shima ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel