Yanzu: Jam'iyyar Labor Party Tayi Kira Da Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa

Yanzu: Jam'iyyar Labor Party Tayi Kira Da Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa

  • Labor Party ta Zargi Legas da Jihar Rivers a Matsayin Jihohi da Ake Ƙwalmaɗa Sakamakon Zaɓe Daga Na Gaskiya Zuwa Na Ƙarya
  • Sun ce Jam'iyyar Dake Mulki A jihohin Sunyi Amfani da Ƴan Jagaliyar siyasa Wajen Hana Su samun Nasara don anga zasuyi Nasara
  • Sun Zargi INEC da Ƙin Daura Sakamakon Zaɓe a Matattarar Manhajar Bayanai ta Yanar Gizo Gizon su, Dalili da Yakawo Shakku a Zuciyar Su

Bayan kammala zaɓukan shugaban ƙasa dana yan majalisar tarayya dana Sanatoci, yanzu haka sakamakon jihohi dana mazaɓu sun soma kammaluwa.

Tuni jam'iyyu suka soma sanin makomar su tare da sanin wace irin rawa suka taka.

Wasu jam'iyyun sunyi abinda ake zato na samun ƙuri'u masu rinjaye a wajajen da suka fi rinjaye.

A yayin da wasu kuma sukayi faɗuwar baƙar tasa.

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Hukumar INEC Tayi Barazanar Soke Zaɓukan Jihar Kogi, Saboda Wasu Dalilai Kwarara

Labor
Yanzu: Jam'iyyar Labor Party ta Peter Obi tayi Kira da Kakkausan Murya Sa'a Hanzarta Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Watakila hakan bai rasa nasaba da yadda sakamakon yazo musu da mamaki, al'ajabi tare da bazata.

Wasu jam'iyyu na ganin sakamakon jam'iyyun suna zuwa ne a salon aringizo , wanda hakan ke kawo shakka akan alƙaluman zaɓukan.

Shakkar ce tasa jam'iyyar Labor Party wacce aka fi sani da LP tayi kira ga INEC data gaggauta sauke zaɓen shugaban ƙasa da akayi jiya.

Ɗaya daga cikin dalilin da jam'iyyar Labor Party ta bayar shine, akwai buƙatar a sauke zaɓen tunda INEC ɗin taƙi ɗaura sakamakon zaɓen a matattarar bayanai ta INEC a yanar gizo gizo.

Shugaban jam'iyyar na ƙasa ne Julius Abure ya bayyana haka a wani saƙo daya rabawa manema labarai, inda tace INEC tasoma saka shakku a cikin zuƙatar al'umma biyo bayan gaza yin haka.

Abure yace, ƙin da INEC tayi na ɗaura sakamakon zaɓe awa goma sha biyu bayan kammala zaɓe abu ne mai cin rai kuma, ba komai bane face fashi da makami irin na siyasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Faɗa Ya Kaure Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

Ya tabbatar da cewa, LP ta ƙadu sosai da yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisa a jihar Rivers.

A cewar sa, gwamnatin jihar tayi amfani da yan daba wajen farmakar rumfunan zaɓe da wajen tattara sakamakon zaɓe.

Ya ƙara da cewa, anyi amfani da ƴan jagaliyar siyasa wajen sace kayan zaɓe da sakamako tare da amfani da BVAS wajen lauya sakamakon zuwa na jabu da ake turawa can babbar ma'ajiyar bayanai ta INEC.

Kamar yadda ya shaidawa gidan talabijin na AIT:

"Muna da alƙaluma na wurare kamar na Obio/Akpor, Khana, Eleme, Obigbo, Rumukoro da sauran wurare inda bayan an fuskanci Labor Party na yin nasara da gagarumin rinjaye akayi musu dirar mikiya aka musu aika-aika aka hana zaɓen faruwa."

Abure ya kuma saka Legas da Delta a matsayin jihohin da ake ƙwalmaɗa sakamakon zaɓe daga na gaskiya zuwa na ƙarya.

Kara karanta wannan

Yadda Masu Kada Kuri'a Sukayi Karanci Basu Fito ba a Kaduna Ya Dame Ni - El-Rufai.

INEC Ta Tsawaita Lokacin Zabe a Jihohi 16?

Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ce ba ta ɗaga lokacin zabe a jihohin Najeriya 16 ba kamar yadda wasu ke yaɗawa, a cewar rahoton .

Wata sanarwa da ta yi ikirarin cewa INEC ta tsawaita lokacin kaɗa kuri'a a zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya na ƙara yaɗuwa a manhajar Whatsapp

Asali: Legit.ng

Online view pixel