Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar da NNPP ta Shigar da Uba Sani

Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar da NNPP ta Shigar da Uba Sani

  • Kotun daukaka kara mai zama a Kaduna ta yi fatali da karar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ranar Laraba
  • NNPP da Suleiman Hunkuyi, sun nemi Kotun ta rushe zabukan fidda gwanin APC na jihar Kaduna domin ya saba doka
  • Lauyan APC kuma tsohon shugaban NBA ya ce wannan babban nasara ce, ya mika godiya ga magoya baya

Kaduna - Kotun daukaka kara mai zama a Kaduna ta yi fatali da karar da jam'iyar NNPP ta shigar tana kalubalantar hukumar zabe INEC, Jam'iyar APC da dan takararta na gwamna, Uba Sani.

Lauyan jam'iyyar APC kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi NBA ta Kaduna, Sule Shu’aibu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sanata Uba Sani.
Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar da NNPP ta Shigar da Uba Sani Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Yace:

"Ina mai farin cikin gaya maku cewa kara mai lamba CA/K/293/2022 da NNPP ta daukaka a nan Kaduna tana tuhumar INEC, APC kuma ta nemi a soke tikitin dan takarar gwamnan APC da yan majalisun jiha 34 an yi watsi da ita."

Kara karanta wannan

2023: Hankula Sun Tashi, Jiga-Jigan PDP 15 Sun Yi Mummunan Hatsari a Hanyar Zuwa Kamfe

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Cikakken bayani kan shari'ar zai zo nan gaba. Yayin da nake taya dukkan mu murnar wannan nasara, ina amfani da wannan damar wurin miƙa godiya ga kowa bisa jajircewa da Addu'a da goyon bayan tawagar lauyoyi."

Yadda shari'ar ta faro a Kotun baya

Vanguard ta rahoto cewa tun farko NNPP da dan takararta na gwamna, Suleman Hunkuyi sun kai karar INEC gaban babbar Kotun tarayya mai zama a Kaduna.

Masu shigar da karar sun kalubalanci matakim INEC ta amincewa da Uba Sani a matsayin dan takarar gwamna na APC da sauran masu neman shiga majalisar jiha 34.

Kotun da yanke cewa NNPP ta makara a wurin shigar da karar domin lokaci ya wuce. Bisa rashin gamsuwa da hukuncin Hunkuyi da jam'iyarsa suka zarce zuwa Kotun daukaka kara.

Kara karanta wannan

Ga Jerinsu da hotuna: Shugaba Buhari Ya Kaddamar Manyan Gine-Gine 7 A Yobe

Masu kara sun zargi cewa APC ba ta gudanar da sahihin taro na zaben Deleget ba, wadanda ke da alhakin kaɗa kuri'a domin fitar da dan takarar gwamna da na majalisar dokokin jiha.

Bisa haka NNPP da Hunkuyi suka shaida wa Kotun cewa bai kamata a ga sunan 'yan takarar APC ba a jerin wadanda INEC ta amince zasu fafata a babban zabe.

Kotu Ta Kori Sanata Elisha Abbo Daga Neman Takara a Inuwar APC

A wani labarin kuma Babbar Kotun Yola ta tsige Sanata Abbo daga matsayin dan takarar APC a mazabar Adamawa ta arewa

Kotun kafa hujja da cewa jam'iyyar APC da yake neman tazarce a inuwarta ta kore shi tun a ranar 7 ga watan Oktoba, 2020.

Alkalin ya bayyana cewa bisa haka Sanatan bai da hurumin samun wata dama ko alfarma da mambobin jam'iyyar APC ke da ikon samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel