Zan Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Da Zaran Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

Zan Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Da Zaran Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

  • Tsohon gwamnan Legas kuma dan takarar shugaban kasa a APC yace zai magance yawan yajin ASUU
  • Bola Tinubu yace idan aka zabe shi ya gaji shugaba Buhari a watan Fabrairu daliban Najeriya zasu dara
  • Shugaba Buhari ya roki yan Najeriya su zabi Tinubu domin zai iya ci gaba da ayyukan sake gina Najeriya

Yobe - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai kawo karshen yawan shiga yajin aikin kungiyar Malaman Jami'o'i ta kasa (ASUU).

Tinubu yace idan aka zabe shi ya zama shugaban Najeriya a zaben watan Fabrairu, 2023 zai samar da bashi ga daliban jami'o'i, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Gangamin APC a Yobe.
Zan Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Da Zaran Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya dauki wadan nan alkawurran ne a wurin gangamin yakin neman zaben APC wanda ya gudana a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku: An Tona Sunan Dan Takarar da Kwankwaso da Peter Obi Suke Wa Aiki a Zaben 2023

Dan takarar ya sha alwashin daidaita bangaren ilimi a Najeriya domin kowa ya samu damar karatu cikin walwala.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan ya kara da cewa zai samarwa manoma da kayayyaki da tallafin noma kuma idan har ya yi nasara zai maida arewa maso gabas ta zama shiyyar fitar da kayayyaki.

Tinubu ya ce:

"Zan fadada wuraren ba da rancen kudi ga ɗaliban jami'o'in Najeriya. Zan tabbata tsarin neman ilimi musamman a jami'o'in ya daidaita ta hanyar magance yawan shiga yajin aikin ASUU."
"Ba za'a sake samun damuwar shiga yajin ASUU ba a jami'o'in mu (idan na zama shugaban kasa)."

Tinubu zai cigaba da aikin da muka fara - Buhari

A wurin kamfen Yobe, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki 'yan Najeriya musamman mazauna jihar su zabi Bola Tinubu ya zama magajinsa a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiya Ta Fito, Dalilin Da Yasa Buhari Ya Zabi Tallata Tinubu A Jihohin Najeriya 10 Kadai

Buhari ya ce yana bukatar mutane su zabi Tinubu ne saboda shi ne mutumin da zai iya ci gaba da ayyukan da ya fara shekaru Bakwai da suka wuce.

"Na rako Bola Tinubu nan ne domin na fada maku ku zabe shi ya ci gaba da manyan ayyukan raya kasa na sake gina Najeriya," inji shi.

A wani labarin kuma kun ji cewa jam'iyyar APC ta rasa tikitin dan takarar Sanata a Mazabar Adamawa ta arewa a zaben 2023

Babbar Kotu a Yola ta tunbuke Sanata Elisha Abbo daga matsayin dan takarar APC a mazabar Adamawa ta arewa a zaben watan Fabrairu.

Alkalin Kotun ya ce tun a watan Oktoba, 2022, APC a gundumarsa dake Mubi ta kore shi, don ba shi ikon tsayawa takara a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel