A Koreni Daga PDP Idan An Isa: Wike Ya Kalubalanci Uwar Jam'iyya

A Koreni Daga PDP Idan An Isa: Wike Ya Kalubalanci Uwar Jam'iyya

  • Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP ya ki ci, ya ki cinyewa ana saur wata guda zabe
  • Bayan fitar Kwankwaso da Peter Obi, Gwamna Wike da wasu gwamnoni biyar sun nakasa kamfen PDP
  • Shi kuwa Atiku ya bayyana cewa ko babu wadannan gwamnonin zai lashe zaben shugaban kasa

Port Harcourt - Gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyar da suka yiwa uwar jam'iyya da dan takararta tawaye watau G5 sun dawo gida Najeriya daga Landan inda suka tafi ganawa.

Dawowarsu ke da wuya, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kalubalanci uwar jam'iyyar ta koresu daga jam'iyyar idan ta isa, rahoton TheNation.

Kana ya karyata rahotannin cewa sun yi yarjejeniya da dan takarar jam'iyyar APC.

Ya ce kawai sun tafi Landan hutawa ne kuma kada wanda ya damu da abinda suka tafi yi.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Mambobin G5 sun hada da Samuel Ortom (jihar Benue),Seyi Makinde (jihar Oyo),Ifeanyi Ugwanyi (jihar Enugu) and Okezie Ikpeazu (jihar Abia).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

wike atiku
A Koreni Daga PDP Idan An Isa: Wike Ya Kalubalanci Uwar Jam'iyya
Asali: UGC

Yace:

"Na tafi kasar waje daren 25 bayan aikin da nayi. Menene ruwan mutane da inda muka je? Ba sun ce sun hakura da mu ba, babu ruwansu da G5."
"Idan zan yi abu, babu bukatar yada jita-jita. Yanzu fa somin-tabi muke yi, babban rikici na nan tafe."
"Sun ce mun gana da wani dan takara. Menen matsalarku da ganawar? Shin Atiku bai ganawa da Gwamnonin APC ne? Ku tambayesa, yana Dubai. shin yana tunanin bamu abinda ke faruwa bane."
"Ko a jiki na. Ku da ke barazanar korarmu kuke tsoro. Mu da ake yiwa barazanar kora ko damuwa bamu yi ba. Ku gwada ku gani idan zaku rayu."

Gwamnan PDP Ya Faɗi Shirin da Tawagar G-5 Ke Kulla wa Game da Babban Zaben 2027

Kara karanta wannan

PDP: Sabon Bayani Ya Fito Yayin Da Gwamna Ortom Ya Magantu Kan Yarjejeniyar Da Aka Ce G5 Ta Yi Da Tinubu

Gwamnan Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya bayyana cewa fafutukar da daidaito da adalci da gwamnonin G-5 ke yi ba don zaɓen 2023 kadai bane.

A cewar, wannan gwagwarmaya da suke yi na tabbatar da adalci ne daga yanzu har zuwa lokacin zaben 2027.

Ya ce abu daya da zai kawo gyara kasar nan shine gaskiya da adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel