Jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Katsina

Jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Katsina

  • Jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Katsina sun yi mubaya'a ga jam'iyyar APC, sun ce Tinubu da Dr Radda za su yi a zabe mai zuwa
  • Rahoto ya bayyana cewa, daruruwan jiga-jigai ne suka fito suka bayyana ficewarsu daga PDP, sun samu tarbar manyan APC a Katsina
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da musayar mambobi yayin da babban zaben 2023 ke karatowa nan gaba kadan

Jihar Katsina - Daruruwan mambobin jam’iyyar PDP ne a karamar hukumar Mashi ta jihar Katsina suka bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Alhaji Ahmad Abdulkadir, daraktan yada labarai na majalisar kamfen APC ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba 14 ga watan Dismaba, PM News ta ruwaito.

Abdulkadir ya ce, wadanda suka sauya shekan sun samu tarbar shugaban APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Daura yayin gangamin kamfen na Dr Dikko Radda a Mashi.

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023" Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Roki 'Yan Najeriya

Mambobin PDP sun koma APC a Katsina
Jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Katsina | Hoto: intelregion.com
Asali: UGC

Alakar Radda da APC, da kuma tasirinsa

Dikko dai shi ne dan takarar gwamnan da ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan APC da aka gudanar a shekarar nan a shirin zaben 2023 mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar daraktan yada labaran:

“Radda ya fara gangamin kamgen dinsa daga mazabar sanata ta Baure a Katsina ta Arewa, mazabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan kaddamar da kamfen dinsa a Faskari, wacce itace mazabar sanatan Katsina ta Kudu.
“Ya zuwa yanzu, dan takarar gwamnan APC ya ziyarci shida daga cikin kananan hukumomi 12 na Katsina ta Arewa. Ya kuma ziyarci sama da unguwanni shida a yankin.”

Radda ya gana da Buhari

Hakazalika, ya shaida cewa, dan takarar gwamnan ya gana shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, inda ya shaida masa halin da al’umma ke ciki da kuma shirinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, Ya Bayyana Magajin Buhari

Dikko ya ce zai kawo ci gaba mai yawa a jihar Katsina matukar aka bashi dama ya zama gwamnan jihar a zaben 2023 mai zuwa, rahoton Daily Post.

Ya kara da cewa:

“Buhari ya yaba da irin kokarinsa ya kuma ba shi kwarin gwiwar cewa tabbas zai lashe zaben badi.”

A fannin tajarar shugaban kasa, dan takarar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babu wanda zai lashe zaben 2023 sai shi da yardar Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel