Gwamna Ya sa an Cafke Baiwar Allah Saboda ta Raba Shinkafa Mara Dadi a Biki

Gwamna Ya sa an Cafke Baiwar Allah Saboda ta Raba Shinkafa Mara Dadi a Biki

  • Wanda ta dafawa mutane abinci mara dadi wajen shagulgulan Kirsimeti a Ebonyi ta shiga hannun hukuma
  • Gwamnan Jihar Ebonyi ya ce ya bada umarni a kama wanda ta aikata wannan laifin domin ayi bincike a kai
  • Gwamnati ta bada kudi a dafawa tsofaffin abinci mai dadi, amma aka kawo abin da aka gagara ci a bikin

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, ya ce ya bada umarnin a cafke mai abincin da ake zargin ta rabawa mutane abinci a wajen wani biki da aka shirya.

A makon da ya wuce aka shiryawa marasa karfi bikin kirismeti na musamman a jihar Ebonyi, The Cable ta ce ana zargin an raba abinci mara dadi.

Da yake bayani a ranar Alhamis, Mai girma David Umahi ya ce an cafke wanda ta bada abincin, kuma da alama sai ta fito da kudin da aka biya ta.

Kara karanta wannan

Aljani Ya Aure ta: Amarya Ta Tubure Tace Bata Yi Ana Tsaka Da Daurin Aurensu Da Angonta

Bayan ya yi Allah-wadai da abin da ya faru, Gwamna Umahi ya shaida cewa za a binciki mai dafa abincin domin daukar matakin da ya cancanta.

Abincin kirismeti bai ciwu ba

A wannan biki da aka shirya domin tsofaffi da zaurawa ganin kirismeti ya zo, ana zargin mai dafa abincin ta rabawa mutane abin da babu wanda ya ci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya nuna cewa wannan mata da aka ba aiki, za ta dawo da kudin da gwamnatin Ebonyi ta biya ta wajen ganin an ciyar da Bayin Allah.

Shinkafa
Dafa dukar shinkafa Hoto: Nanaba Kitchen
Asali: UGC

Domin ganin an sa dattawan farin ciki a irin wannan lokaci, Gwamnan ya ce za a sake shirya wani bikin, kuma zai sa ido a kan abincin da za a raba.

Aminiya ta rahoto David Umahi yana bayanin muhimmancin kula da tsofaffin a addinin kirista, ya ce yin hakan zai sa rayuwar mutum tayi albarka.

Kara karanta wannan

Gwamna ya Umarci a Damke Kukun da Tayi Abincin Liyafar Kirsimati da ya Shirya, Yace Babu Dadi

Za a sake yin bikin yau ko gobe

“Saboda haka za mu maimaita wannan biki domin mu taya iyayenmu maza da mata murna.
Littafin Injila ya yi umarni gare mu da mu karrama iyayenmu maza da mata domin mu yi tsawon rai a Duniya.
Ina so in yi tsawon rai a doron kasa domin na sha wahala tun daga lokacin da nake matashi."

- David Umahi

An raba turamen zani na banza

Baya ga batun abinci, Gwamnan na Ebonyi bai ji dadin turmin zanin da aka rabawa tsofaffin da zaurawan jihar ba, ya ce ba irinsa aka rabawa ma’aikata ba.

An rahoto Umahi yana cewa ‘yan kwangila su shirya shigo da turamen zannuwa 10, 000 masu kyau da za a rabawa dattawa da marasa mazajen da ke jihar.

Za su kashe ni - Ejike Agbo

An ji labari Ejike Agbo wanda ya nemi zama ‘dan takaran majalisar dokoki na Kudancin Ohakwu, amma aka doke shi a zaben tsaida gwani, ya je kotu.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Abubuwa 2 da ya Zama Wajibi Magajin Buhari Ya Yi Yaki da Su a Mulki

Zuwan ‘dan siyasan kotu domin ya yi karar jam’iyya mai mulki da ‘dan takaransa, ya sa shi da iyalinsa ba su zaune cikin zaman lafiya, ana neman kashe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel