Gwamna Yayi Umarni Cafke Kukun da Tayi Abincin Liyafar Kirsimeti, Yace Babu Dadi

Gwamna Yayi Umarni Cafke Kukun da Tayi Abincin Liyafar Kirsimeti, Yace Babu Dadi

  • Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi yayi Allah wadai da abincin liyafar da ya hadawa matan da mazansu suka rasu da tsofaffin jihar na Kirsimati
  • Tuni Gwamnan yayi umarni a kama kukun da aka ba kwangila kuma a dawo masa da kudinsa sannan zai sake shirya wata liyafar don tsofaffin su more
  • Umahi ya kushe nagartar zannuwan da aka rabawa matan da mazansu suka mutun da tsofaffi inda yace za a sake raba nagartattu guda 10,000

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, yace yayi umarnin kama wata mai dafa abinci da aka yi hayarta kan zargin bada abinci mara dadi ga matan da mazajensu suka rasu da kuma dattawa a wata liyafar Kirsimati a jihar.

Abincin Kirsimeti
Gwamna Yayi Umarni Cafke Kukun da Tayi Abincin Liyafar Kirsimeti, Yace Babu Dadi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto, an kama kukun ne a ranar Alhamis a wurin liyafar da Gwamnatin jihar Ebonyi ta hada.

Kara karanta wannan

2022: Mai Kamfanin BUA Ya Samu Cigaba, Shine na 4 a Jerin Masu Arzikin Afrika

Ku biya ni kudin, Umahi

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, Umahi ya kushe lamarin inda yace bai dace ba a ciyar da jama’a abinda ba za a iya ci ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace za a binciki kukun yadda ya dace kuma yace a biya shi kudin da ya kashe kan abincin.

“A don haka, zamu sake maimaita liyafar saboda mu yi shagalin murna tare da iyayenmu maza da mata.”

- Yace.

“Injila ta bukaci mu girmama iyayenmu mata da maza yadda zamu yi tsawon rai a duniya.
“Ina don Samun rayuwa mai tsawo saboda na sha wahala lokacin ina matashi.”

TheCable ta rahoto cewa, Gwamnan yace da kanshi zai duba abincin matan da mazajensu suka mutu da tsofaffi a shagali na gaba.

Yace zannuwan da aka raba musu ma basu da inganci.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Najeriya Suka Share Hawayen Wata Dattijuwa Da Ke Kwana a Titi, An Sama Mata Muhalli

“Dole ne mu yi shagalin a ranar 20 ko 21 yayin da duk wanda ya cuta wadannan mutanen ya shiga matsala.”

- ya kara da cewa.

“Mutanen da suka samar da na ma’aikatan gwamnati su shirya kawo zannuwa masu nagarta guda 10,000 ga matan da mazajensu suka rasu da dattawa.
“Lokacin da na bayyana cewa irin tada kayar bayan da wasu jama’ar yankin zasu yi sai an kasa shawo kanshi idan ba a duba ba, jama’a basu mayar da hankali ba.
“Ebonyi ba za ta taba zama cikin wani rikicin tada kayar baya ba wanda zai kawo kashe-kashe da lalata kadarorin jama’a.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel