Daga Rushe Filayen N30m, Mutum 10 a Jihar Delta Sun Rasu Ta Dalilin Bugun Zuciya

Daga Rushe Filayen N30m, Mutum 10 a Jihar Delta Sun Rasu Ta Dalilin Bugun Zuciya

  • An samu tashin tashina a jihar Delta yayin da wasu masu filaye suka fito kan titi don yin zanga-zanga bisa kwacewa da rusa gine-ginensu
  • Wannan mummunan yanayi dai ya kai ga wasu mutum 10 masu filaye sun mutu, lamarin da ya jawo cece-kuce
  • Yayin da suke zanga-zangar, sun yi kira ga gwamnan jihar Okowa da ya dawo musu da filayen da suka zuba miliyoyi a kai

Asaba, jihar Delta - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, akalla mutum 2,000 ne suka fito zanga-zanga don nuna adawa da yadda gwamnati ta kwace tare da ture gine-ginensu.

Sun bayyana cewa, akalla mutum 10 sun mutu sakamakon rushe wadannan gine-gine da darajarsu ta kai akalla N30bn.

An ruwaito cewa, filayen na can a kusa da filin jirgin Asaba na kasa da kasa, kuma sun sun siya filayen ne daga mazauna unguwar Umuodafe a yankin Ibusa ta karamar hukumar Oshimili a jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Sheke Tsohuwa Mai Shekaru 120 tare da Wasu 5

‘Yan zanga-zangar sun bayyana kukan cewa, a yanzu gwamnatin jihar Delta ta kwace filayen tare da bayyana hakan a hukumance.

Gwamnatin jiha ta kwace filayen jama'a, sun shiga tashin hankali
Daga Rushe Gidan Na N30m, Wani Mutum a Jihar Delta Ya Rasu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ga masu zanga-zangar dauke da alluna suna kira da gwamna Okowa na jihar ya dawo musu da hakkinsu da aka wace.

Masu filaye sun fito zanga-zanga

Da yake magana a madadin masu zanga-zangan, wani mutum Mr Raymond Ifeanyi ya koka da yadda aka kwace filayen ba bisa ka’ida ba, kuma ya ce laifin gwamna Ifeanyi Okowa ne.

Ya shaidawa Punch cewa:

“Mun sayi wannan filin tun 2018, abin mamaki suka zo da motar rusau kana suka fara rusa gine-ginenmu, cewa wai gwamna Okowa ya karbi filin.
“Boko Haram sun lalata gida na a Arewa, don da dan abin da nake dashi, na so Asaba na siya filin kuma na fara gini ta yadda ahali na za su zama matsuguni.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: An Sake Samun Ibtila'in Fashewa a Babban Birnin Wata Jiha a Najeriya

“Amma suka kawo motar rusau kana suka rusa gine-ginen da suka kai N30bn. Mun bi duk wata ka’ida wajen mallakar filin daga mazauna yankin kuma muna da takardu.”

Mun zuba kudade da yawa, inji masu filayen

Wani daga cikin masu filayen, Engr. Akeen Lassi da wata Mrs Juliana Ogbuagwu sun kuka da yadda suka saka sama da N200m wajen raya wurin, tare da cewa sun siya filayensu ta hanyar da ta dace.

A cewarsu:

“Sai da muka nemi bayani game da filin kadin mu siya. Fili ne sakaka, mun ziyarci ma’aikatar filaye kuma an tabbatar mana babu wata matsala daga gwamnati kafin mu siya daga mazauna."

Sun kuma yi karin bayani da cewa, akalla mutane 10 ne suka mutu saboda bugun zuciya bayan kwace filayen.

Martanin wani kwamishina a jihar

Kwamishinan yada labarai na jihar, Mr Charkes Aniagwu ya bayyana cewa, an karbi gaba dayan filin ne saboda biyan bukatun ayyukan al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

AbdulJabbar Kabara: Abubuwan da suka faru aka yanke masa hukuncin kisa

A cewarsa:

“A wancan fili da ake magana, gwamnati tun tuni kafin yanzu ta mallake shi domin ayyukan al’umma."

Gwamnatocin jihohi sun sha kwace filayen jama'a, a shekarar 2021 gwamnatin Kano ta ce ta kwace filaye 400 daga hannun mutanen jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel