Gwamnatin Kano Tace ta ƙwace filaye kimanin 400 daga Hannun Mutane
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta ƙwace filaye 400 daga hannun wasu mutane ta maida ma asalin waɗanda suka mallake su
- Shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci na jahar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne ya sanar da haka a hedkwatar hukumar
- Ya kuma ƙara da cewa sun ƙwato maƙudan kuɗaɗe da aka karkatar dasu ta hanyar da bata dace ba a cikin wannan shekarar.
Hukumar dake kula da ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci ta jahar Kano (PCACC) ta ƙwace filaye kimanin 400 daga hannun wasu mutane a faɗin jihar.
KARANTA ANAN: Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta
Ta kuma bayyana cewa yawan filayen ta ƙwace su ne ta maidama asalin waɗanda suka mallaki filayen, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana haka a wani taron haɗin guiwa da ya gudana a hedkwatar hukumar ranar Laraba.
Shugaban ya ƙara da cewa hukumarsa ta ƙwato maƙudan kuɗaɗe da suka wuce N521,964,122.
Rimingado, ya bayyana cewar hukumar su ta samu korafe-korafe 2256 daga wajen jama'a cikin wannan shekarar da muke ciki.
Ya ce hukumar ta samu nasarar gano wuraren ajiya inda aka ajiye kayayyaki masu muhimmanci na biliyoyin nairori da aka kwace amma daga baya aka sake su bayan tattaunawa da yan kasuwar.
KARANTA ANAN: Abun farin ciki: Ma’aurata na shirin tarban dansu na fari bayan shekaru 25 da aure
Rimingado yace:
"Mun kwato filaye 400 daga hannun wasu mutane kuma mun maida su ga asalin waɗanda suka mallaki filayen a sassa daban-daban na jihar nan."
"Mun kuma shiga tsakani, mun sulhunta matsalolin tsaro 60 tsakanin makiyaya da manoma, wanda mafi yawancin su a kan kiyo ne."
Rimingado yace dayawan mutane ana kaisu kotu kan rikicin da basu ji ba basu gani ba, musamman a ƙananan hukumomin Ɗanbatta, Ɓagwai da Kuma Tudun Wada.
Ya kuma ƙara jaddada cewa hukumar su zata cigaba da aiki yadda yakamata don ƙara tabbatar da Kano a cikin jihohin farko a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa.
A wani labarin kuma Gwamnatin Najeriya ta na neman haramta kawo motar da ta shekara 7 a Duniya
Kwastam ta kawo shawarar a daina shigo da motocin da su ka yi rugu-rugu. Shugaban Hukumar ya na so a hana shigo da motar da aka hau na shekara 7.
Shugaban hukumar, Hameed Ali ya ce kudin da jami’an hukumar kwastam su ke samu ya ragu.
Asali: Legit.ng