An Sake Samun Fashewa Babbar Tanka a Babban Birnin Jihar Oyo

An Sake Samun Fashewa Babbar Tanka a Babban Birnin Jihar Oyo

  • Wata babbar Motar dakon man Fetur ta fashe kuma ta kama da wuta daga baya ta tarwatse a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
  • Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne lokacin da Tankar ta kucce wa diraban ta yi kan wasu shaguna a kusa da gidan Man NNPC
  • Jami'an hukumar kashe wuta sun isa wurin a kan lokaci kuma kakakin yan sanda yace sun tura dakaru wurin

Ibadan, Oyo - Wata babbar Tankar Man Fetur ta kama da wuta bayan ta fashe a Apata junction kan Titin Ibadan/Abeokuta, a jihar Oyo ranar Alhamis.

Jaridar Punch ta rahoto cewa lamarin ya auku ne yayin da Tankar dakon man ta kucce wa direban kuma ta yi birki da wasu shaguna da ke gefen gidan Man NNPC kafin daga bisani ta watse filla-filla.

Kara karanta wannan

Da walakin: Ra'ayoyin jama'a game da hukuncin da aka yankewa Sheikh Abduljabar

Fashewar Tanka a Ibadan.
An Sake Samun Fashewa Babbar Tanka a Babban Birnin Jihar Oyo Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda wuta ta kama rigi-rigi yayin da waɗanda suka ga faruwar lamarin suka soma kururuwar neman a kawo ɗauki.

A halin yanzun, jaridar The Nation ta tattaro cewa tuni jami'an hukumar kashe gobara suka isa wurin mintuna kaɗan bayan faruwar lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har zuwa yanzun da muka haɗa wannan rahoton, Babu sahihin bayani kan adadin mutanen da mai yuwuwa suka rasa rayukansu ko suka jikkata sakamakon lamarin.

Sai dai an ce wutar da ta kama bayan fashewar tankar ta yaɗu zuwa wasu gine-gine da ke kewayen yankin baya ga shagudan wurin.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Ya bayyana cewa shugaban Caji Ofis din yankin watau DPO ya tura jami'ai zuwa wurin domin kai ɗauki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Harbe Daraktan Kwamitin Kamfen Atiku A Wata Jiha

Jim Kadan Bayan Dawowarsa Bakin Aiki, Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Murkushe Wata Mota

A wani labarin na daban kuma mun kawo muku Yadda jirgin kasa Abuja-Kaduna ya murkushe wata mota da ta hau kan titinsa

Jirgin ƙasa mai aikin jigila daga Kaduna zuwa Abuja ya murkushe wata mota dake tsaye kan titinsa a a yankin Kubwa, babban birnin tarayya Abuja.

Wasi Hotuna da suek yawo sun nuna yadda mutane suka mamaye wurin, wasu na aikin ceto wssu kuma sun je ba idonsu abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel