‘Yan Bindiga Sun Halaka Tsohuwa Mai Shekaru 120 a Duniya

‘Yan Bindiga Sun Halaka Tsohuwa Mai Shekaru 120 a Duniya

  • ’Yan bindiga sun yi dirar mikiya anguwar Raka cikin karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto tare da barin rudani da firgici a zukatan mazauna yankin
  • Kamar yadda hakimin Raka ya bayyana, 'yan ta'addan sun halaka wata tsohuwa mai shekaru 120 da wasu biyar gami da kone gidajensu da dama kurmus
  • Duk da basu yi nasarar sace kowa ba, amma an ruwaito yadda suka sace kayayyakin abinci sannan da shanun mazauna yankin

Sokoto - A ranar Talata 'yan bindiga sun halaka wata tsohuwa mai shekaru 120 da wasu biyar tare da kone gidajensu tare da sace musu dabbobi a Sokoto, jaridar Leadership ta rahoto.

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga Sun Halaka Tsohuwa Mai Shekaru 120 a Duniya. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun labartawa manema labarai yadda 'yan bindiga sun yi dirar mikiya anguwar Raka cikin karamar hukumar Tangaza, in suka jefa firgice da rudani a zukatan mutane bayan sun tafi.

Kara karanta wannan

Da walakin: Ra'ayoyin jama'a game da hukuncin da aka yankewa Sheikh Abduljabar

Kamar yadda hakimin Raka, Sa'idu Wakili ya bayyana:

"Duk da babu wanda aka yi garkuwa da shi, 'yan bindiga sun halaka mutane shida duk da wata tsohuwa, sannan suka kone kashi biyu cikin kashi uku na gidajen anguwar, yayin da suka sace kayayyakin abinci da shanun jama’a.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci mazauna yankin da su roki Allah ya kawo musu daukin gaggawa don zaman lafiya ya tabbata, sannan yayi kira ga jihar da gwamnatin tarayya da su yi kokari wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin.

Shugaban karamar hukumar Tangaza na rikon kwarya, Ibrahim Lawal Junju, tare da mai bada sharawa ta musamman a bangaren kula da titina, Injiniya Mai Damma Tangaza, ya jajanta tare da mutanen anguwar Allah ya kyauta.

Sun siffanta harin a matsayin ba-zata tare da alkawarin zuwa ga gwamnatin don bada taimakon da ya dace ga wadanda lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Halaka Abu Na-Iraqi da Abu-Na Masari, Gawurtattun 'Yan Ta'addan da Suka Addabi Katsina

Katsina: ‘Yan Sanda sun Sheke manyan ‘yan bindiga da aka dade ana nema

A wani labari na daban, jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun halaka fitattun ‘yan bindiga da aka dade ana nema ido rufe.

Lamarin ya faru ne bayan sun kai farmaki kwatas din Rima dake Dutsinma-Ma a jihar Katsina.

Samun kiran gaggawa ne yasa ‘yan sandan suka tarar da Abu-Na Iraqi da Abu-Na Masari inda suka yi musu ruwan wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel