Jam'iyyar PDP Tace Kamata Yayi ace Tinubu Yaje Ya Huta Ya Jiira lokacinsa

Jam'iyyar PDP Tace Kamata Yayi ace Tinubu Yaje Ya Huta Ya Jiira lokacinsa

  • Jam'iyoyi a Nigeria na sukan junan su da maganganu kala-kala kan dacewa ko akasin haka, musamman kan batun zaben 2023
  • Ko satin da ya gabata 'dan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zargi sauran 'yan uwansa yan takara da gazawarsu a fannoni da dama na tafiyar da shugabanci
  • Jigo a jam'iyyar PDP, kuma mai magana da yawun 'dan takarar shugaban kasa Sen Dino Malaye yace Tinubu yai tsuffan da bazai iya mulkar Nigeria ba

Abuja: Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Tinubu da ya daina takara yaje huta.

A martanin da Tinubu ya yi a baya ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya janye daga takarar saboda ya sha tsayawa takara kuma ya gaza kaiwa ga gaci.

Kara karanta wannan

Ta Ya Ka Tara Dukiyarka Idan Gidanku Talakawa Ne? Atiku Ya Aika Sako Ga Tinubu

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, a ranar Juma’a ya ce idan har akwai. duk wanda ya kamata ya huta, tsohon gwamnan jihar Legas ne. kamar yadda jaridar Tribune ta bayyana

Da yake magana a wani taron tattaunawa da ‘yan jarida a Abuja, ya lura cewa, Tinubu ba ya cikin yanayin lafiya mai kyau da kuma yanayin tunani da zai jagoranci kasar nan kamar yadda ya ke nunawa a kullum.

Bola tinubu
Jam'iyyar PDP Tace Kamata Yayi ace Tinubu Yaje Ya Huta Ya Jiira lokacinsa Hoto: Tribune
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Makogwaron PDP yace?

Kakakin jam’iyyar ya ce:

“Ban sani ba ko shi ma ya shawarci kansa. Idan akwai wanda yake bukatar ya huta, shi ne.
“Na biyu, shi ne mutum daya tilo da ya karya tsarin mulkin kasa ba. Za ku tuna yakin neman zabensa a jihar Delta. Ya ce dan takarar jam’iyyar APC a jihar Delta ne zai zama gwamnan jihar Neja Delta.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Rasa Jiga-Jigan Yakin Neman Zabensa A Yankin Arewa Maso Gabas

“Don haka, idan akwai wanda ke bukatar hutawa, shi ne. Mutum ne da ko da yake ba ya iya furta wata kalma, yana ta girgiza, ba zai iya ba.
“A Legas, ya ce ‘Kuna sona? to kuje ku karbo APV.' kamar yadda yadda zaka ga Asiwaju yin wasu abubuwa na sabawab ka'idar magana".

“Amma ina ganin idan wani yana bukatar shawara ya huta, to shi ne kuma ina fatan nan ba da jimawa ba zai huta domin baya da karfin jiki, da tunanin da ake bukata na zama shugaban kasa a kasar nan, akwai sauran batutuwa. wanda na yi imani jama'a zasu sheda kan batun nan".

Shima da yake magana a tatttaunawa da ‘yan jarida a Abuja ranar Juma’a, Darakta-Janar a Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugabancin Jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da dalci a zabe 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel