‘Yan Bindiga Sun Sace Mata, ‘Ya ‘Ya da Wasu Makwabtan ‘Dan Majalisa a Najeriya

‘Yan Bindiga Sun Sace Mata, ‘Ya ‘Ya da Wasu Makwabtan ‘Dan Majalisa a Najeriya

  • A daren yau ne wasu ‘yan bindiga suka shiga gidan Hon. Aminu Ardo Jangebe, suka yi barna
  • Aminu Jangebe yana wakiltar mutanen mazabar Talata Mafara ta Kudu a majalisar dokokin Zamfara
  • ‘Yan bindigan sun dauke matar ‘dan majalisar da ‘ya ‘yansu hudu, sannan suka sace makwabtansa

Zamfara - Labarin da muke samu daga jihar Zamfara bai da dadi, ana zargin ‘yan bindiga sun yi awon gaba da iyalin Aminu Ardo Jangebe a gidansa.

Jaridar Punch tace a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba 2022, wasu miyagu suka kutsa gidan Honarabul Aminu Ardo Jangebe, suka dauke mutane.

Aminu Jangebe ‘dan majalisa ne mai wakiltar Talata Mafara ta kudu a majalisar dokoki.

Wata majiya ta shaida cewa da ‘yan bindigan suka shiga garin da kimanin karfe 11:00 na daren Juma’a, sai suka rika buda wuta domin su tsorata kowa.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne

An tada hankalin jama'a - Mazauni

Sani Abubakar wanda mazaunin garin ne yace da jin harbi, mutane suka yi ta gudu, wadanda ke cikin gidajensu kuma suka rufe domin gudun a dauke su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Sani Abubakar, kai-tsaye ‘yan bindigan suka wuce gidan ‘dan siyasar, suka balla kofar.

‘Yan Bindiga'
'Yan Sanda a bakin aiki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Bayan balla kofar sai suka samu damar kutsawa cikin gidan, suka dauke matar Aminu Jangebe da wasu ‘ya ‘yansu hudu, sai suka yi gaba da su.

An hada makwabtan Honarabul

A hanyar fitowa daga gidan Honarabul Jangebe, sai ‘yan bindigan suka ci karo da wasu makwabtansu, haka zalikasuka hada da wadannan mutane.

An bada sunan makwabtan ‘dan majalisa da tsautsayin ya auka da su da Malam Yahaya da Malam Sa’adu Mainama, har zuwa yanzu babu labarinsu.

Baya ga haka, mazaunin garin da aka yi hira da shi, yace ‘yan bindigan sun tsere da wani babur da ake zargin na daya daga cikin mutanen da aka sace ne.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

BBC Yoruba ta tabbatar da wannan labari kamar yada Kwamishinan yada labarai na Zamfara, Alhaji Ibrahim Dosara ya shaidawa BBC Hausa a yau.

Kakakin ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu yace zai fitar da jawabi a kan lamarin. Har zuwa yanzu da ake hada rahoton, Shehu bai ce komai ba.

An wulakanta Abu Giza

Kun ji labari ana rade-radin cewa Shugaban APC na kasa aka tubewa kaya da ya je mahaifarsa a jihar Nasarawa da aka je yin wani gagarumin taron siyasa.

Amma bayanai daga bakin Shugaban majalisar IPAC ya nuna wani daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a Nasarawa aka ci wa mutunci ba shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel