Pastor Remi Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Yi Shugaban Kasa Da Mataimaki Duk Kirista A Nigeria

Pastor Remi Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Yi Shugaban Kasa Da Mataimaki Duk Kirista A Nigeria

  • Har Yanzu kura bata lafa ba game da takarar muslmi da musulmi da jam’iyyar APC tayi a Duniyar siyasar Nigeria.
  • Dalilin takarar muslmi da musulmi, jam’iyyar APC ta rasa tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawan da Yakubu Dogara tsohon kakakin majalissar wakilai
  • Tinubu dai ya dage kan wannan matsayar tasa, inda yace nasarar 1993 ce ke tattare da takarar tasu

Lagos: Uwargidan 'dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Oluremi Tinubu tace kada kiristocin Nigeria ko kuma masu damuwa su damu, domin nan gaba za’ai shugaban kasa kirista haka mataimakinsa ma

Uwargidan na wannan jawabin ne a wajen yakin neman zabensu wanda mata suka shirya.

Olowaremi
Pastor Remi Tinubu Tace Nan gaba za a yi shugaban kasa da mataimaki duk Kirista a Najeriya
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Oluremi Bola Tinubu ta kasance mata ga Bola Ahmed Tinube Kuma Fasto ce da take bin 'darikar katolika a Nigeria. Rahotan BBC Hausa

“Allah ne kadai yasan'kulle-'kulle da mutane sukeyi game da takarar mijina da Shettima, amma muna tare da Allah shine zai mana komai.” Inji Remi
“Mijina ya za'bo Shettima ne dan ya canja fasalin yadda siyasa take da yadda ake kallonta a Nigeria”

Kalaman Remi dai na zuwa ne a jihar Legas, a yayin yakin neman zaben da mata magoya bayan jam’iyyar suka shirya, kuma suke gudanarwa.

Ana yawan samun korafe-korafe daga mutane da dama daga addinin kirista ko musulunci kan takarar musulmi da musulmi da jam’iyyar APC tayi inda mutane da dama ke ganin lamirin bai dace ba ko ka'dan.

Waiwaye Game Da Irin Wannan Batun Game Da Takarar Musulmi Da Musulmi tarihin Siyasar Nigeria ta 1993

A Shekarar 1993, an ta'ba gwada tsarin 'dan takarar shugaban kasa musulmi da musulmi inda ya samu gaggarumin rinjaye wanda Cif MKO Abiola yai takara a wancan lokacin yayin da Kingibe yai masa mataimaki.

To sai dai shugaban mulkin soji na wancan lokacin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya soke za'ben tare da mika mulkin rikon kwarya ga Cif Ernest Shonekan mulki, wanda Abacha ya ham'barar da shi a shekarar 1993

Asali: Legit.ng

Online view pixel