Wasu ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Shugaban Majalisar Kamfen PDP Na Jihar Ribas

Wasu ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Shugaban Majalisar Kamfen PDP Na Jihar Ribas

  • Rahoton da ke iso mu ya bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki wani jigon jam'iyyar PDP a cikin gidansa
  • Rahoto ya ce, an lalata motoci da dama yayin da aka fasa kofar gidan sanatan aka kutsa don aikata mummunan barna
  • Ana kyautata zaton abokan adawar siyasa ne suka kitsa wannan lamari, amma ba a bayyana su wanene ba

Jihar Ribas - Wasu da ake zargin ‘yan bangan siyasa ne a ranar Alhamis da safe sun farmaki gidan sanata Lee Maeba a unguwar GRA Phase 3 da ke Fatakwal a jihar Ribas.

Maeba ne shugaban majalisar kamfen na Atiku da jam’iyyar PDP a jihar ta Ribas, inji rahoton jaridar Punch.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa, wasu tsagerun ‘yan daba ne suka shigo gidan sanatan, inda suka yi harbi tare da yin kaca-kaca da kofar gidan kafin su shiga.

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: Fitaccen sarkin da 'yan bindiga suka sace a wata jiha ya shaki iskar 'yanci

Yadda aka farmaki gidan na gaban goshin Atiku
Wasu ’Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Shugaban Majalisar Kamfen PDP Na Jihar Ribas | Hotuna: Atiku Abubakar, Nyesom Wike
Asali: Twitter

An ruwaito cewa, sun lalata motoci biyar, ciki har da wata kirar Jeeep yayin da mutum uku da ke cikin gidan, ciki har da dangin sanatan suka gudu domin tsira da rayukansu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da wakilin jaridar jaridar ya ziyarci wurin da misalin karfe 10:50 na safe, ya ga an kawo jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS da ‘yan sanda, Within Nigeria ta tattaro.

An ga lokacin da jami’an tsaron suka dauki sanatan daga gidansa zuwa wani wurin daban da ba a bayyana ba.

A tun farko, akwai rikici tsakanin gwamnan jihar Ribas da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Gwamna Wike ya waiwayi gwamnonin yankin Neja-Delta, ya caccake su

A bangare guda, yayin da rikicin Atiku da Wike ke kara kamari, gwamnan na jihar Ribas ya bukaci gwamnoni 5 na yankin Neja-Delta da su daina sukarsa.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: 'Yan sanda sun ceto wasu mutum uku da aka sace jiya da dare a Abuja

Wani rahoto ya bayyana cewa, gwamna Wike ya yi magana ne game da bashin kudin da gwamnatin ta biya gwamnonin kwanakin baya.

A maimakon sukarsa, ya ce idan ba tsoro ba su dauki makwanni uku suna kaddamar da ayykan da suka yi a jihohinsu.

Ya kuma bayyana cewa, idan suka son sukarsa, su cire tsoro su yi kai tsaye ba sai sun fake da wasu kungiyoyi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.