Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 8, an Kone Gidaje 47 a Borno

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 8, an Kone Gidaje 47 a Borno

  • An samu sabani mara dadi tsakanin manoma da makiyaya a jihar Borno, an yi asarar rayuwa sama da 5 a rikicin
  • Hakazalika, an ruwaito yadda aka kone gidaje sama da 40, lamarin da ya jawo shiga tsakani daga hukumomin tsaron jihar
  • An zauna zaman sulhu, hukumomin tsaro da manyan ma’aikatan gwamnati sun zauna don dinke barakar

Maiduguri, jihar Borno - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar ya ce akalla mutane takwas aka kashe tare da kone gidaje 47 a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya saboda shiga gonaki a karamar hukumar Bayo ta jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 3 Disamba, 2022 a wani taron da shuganannin kungiyar Miyetti Allah da ta manoma a birnin Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Amimu ya shaki iskar 'yanci: Yadda aka mika matashin ga iyayensa daga magarkama

Ya bayyana cewa, mutane takwas da aka kashe sun hada da kananan yara uku, inda yace lamarin ba karamin abin damuwa bane ga hukumomin tsaro a jihar.

Makiya da manoma sun yi fada, an kashe mutane da dama
Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 8, an Kone Gidaje 47 a Borno | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya kuma shaida cewa, a karshen taron da aka gudanar, za a samar da hanyoyin dike barakar ta hanyar sanya ido kan makiyaya da ke kaura a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umar ya bayyana cewa, an kama wasu da ake zargi da hannun a wannan aika-aikata, kuma an kaisu kotu domin gudanar da bincike da kuma hukunta masu laifi.

Wadanda suka halarci taron

An ruwaito cewa, wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin hukumomin tsaro, manyan jami’an gwamnati da shugabannin kungiyoyin biyu da suka samu sabani.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah MACBAN, Ahmadu Musa-Karube ya ta’allaka faruwar lamarin ga yawaita nome hanyoyoyin shanu a cikin dazuka, Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

“Shanu ba firewa suke ba, dole su samu hanyar wucewa, amma sau tari za ku ga manoma sun nome hanyoyin shanu. Magana ta gaskiya, akwai bukatar magance hakan cikin gaggawa.”

Kara karanta wannan

Hukumar Sojojin Kasa Tace Zata Canja Fasalin Kai Hare-Hare A Fadin Nigeria

Har ila yau, wakilin manoma, Hassan Musa, shi ma yace tabbas za a daina noma hanyoyin shanu, amma akwai bukatar gwamnatin jihar ta haramta kiwo cikin dare.

Ana yawan samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya, musannan a karshen damina lokutan da ake dauke amfanin gona.

Makamancin irin wannan rikicin ya faru a jihar Kano, inda aka samu asara da yawa a wasu kayuka sama da 10 a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel