Dalla-Dalla: Yadda Aka Mika Aminu Muhammad Ga Iyayensa Bayan Dauko Shi Daga Magarkama

Dalla-Dalla: Yadda Aka Mika Aminu Muhammad Ga Iyayensa Bayan Dauko Shi Daga Magarkama

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an sako Aminu Muhammad tare da mika shi ga iyayensa bayan shafe kwanaki a hannun jami’an tsaro
  • Ana zargin Aminu da zagin uwar gidan shugaban kasa a shafin Twitter, wannan yasa aka tarnake shi a wata magarkama da ke Suleja a jihar Neja
  • A tun farko daliban Najeriya sun yi barazanar girgiza Najeriya da zanga-zanga kan lamarin da ya faru da Aminu matukar ba a sako shi ba

FCT, Abuja - Rahotanni sun karade Najeriya na yadda uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ya amince da janye kara tare da kashe maganar cin zarafin da ta shigar kan wani matashin dan makaranta.

Bayan haka ne kuma iyayen dalibin da sauran daginsa suka bayyana dalla-dalla yadda aka ba da umarnin sakinsa tare da kashe maganar ba tare da sake dago ta ba.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Dai Aminu Zai Gana Da Shugaba Buhari A Villa Yau, Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar Data Shigar

Idan baku manta ba, Aminu Muhammadu, dalibi a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya fito shafin Twitter ya yi kalaman gatsali ga uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari.

Yadda aka sako Aminu Muhammad daga hannun jami'an tsaro
Dalla-dalla: Yadda aka mika Aminu Adamu Muhammad hannun iyayensa daga magarkama | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Wannan yasa aka kamo shi daga jihar ta Jigawa, aka shilla dashi Abuja domin gurfanar dashi a gaban kotu bisa laifin bata sunan uwar gidan shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sako Aminu

Wani wakilin BBC Hausa ya bibiyi lamarin don gano halin da ake ciki, da kuma tabbatar da maganar sakin matashin daga iyayensa.

A wani sakon murya da Legit.ng Hausa ta samo daga BBC Hausa da ke bayyana yadda aka sako matashin, an ce tuni aka ba warware batun karar tare da mika matashin ga iyayensa.

A cewar sautin muryar, an dauko Aminu daga magarkamar Suleja inda aka ajiye shi tare da zarcewa dashi ofishin kwamishinan ‘yan sandan yankin babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

An ruwaito cewa, an ga Aminu tare da ‘yan sandan da ke Abuja da shugaban kungiyar daliban Najeriya (NANS) Usman Barambu.

An ga Aminu cikin damuwa da tsoro

A cewar majiyar, an ga Aminu cikin damuwa da gajiya, alamun da ke nuna har yanzu yana cikin wani yanayi na tashin hankali.

A cewar iyayensa, wannan ba zai rasa nasaba da tsare shi da aka yi na tsawon kwanaki ba, kuma haka suna hana dan jarida tattauna da matashin kan halin da ya shiga.

Sun bayyana bukatar a ba dan su damar ya huta tukuna kafin a fara yi masa duk wasu tambayoyin abubuwan da ya gamu dasu daga kama shi zuwa sakinsa.

A cewar rahoto, Yaya Isa, wani aminin mahaifin Aminu ya karbo shi daga hannun ‘yan sanda, kuma daga nan ya zarce dashi gida.

A cewar Yaya Isa:

“Gaskiya an saki Aminu kuma yanzu haka Aminu yana tare da mu yana gida. Mu a matsayinmu na iyayen yaro, za mu yi masa magana kada ya sake irin wannan abu ba ma a uwar gidan shugaban kasa ba, a kan kowa ma, Insha Allahu ba za a sake yinshi ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uwargidan Shugaban Kasa ta Huce, Ta Janye Karar Dalibin da ya ‘Zageta’

“Ga ‘yan Najeriya da suka taya mu jajen wannan al’amari muna musu godiya kuma Allah ya kare ya tsayar da abin haka.”

A tun farko kun ji cewa, kungiyar dalibai ta Najeriya ta ce za ta rikita kasar nan da zanga-zanga idan aka gaza sako Aminu kafin 5 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel