Gwamnati Bata Son Kawo Karshen Ta’addanci, Turji Ya Fallasa Masu Morewa Daga Rashin Zaman Lafiya

Gwamnati Bata Son Kawo Karshen Ta’addanci, Turji Ya Fallasa Masu Morewa Daga Rashin Zaman Lafiya

  • Gogarman ’dan bindiga, Bello Turji, ya sanar da cewa gwamnatin Najeriya bata son kawo karshen ta’addanci saboda jami’ai suna amfana da shi
  • Turji ya sanar da cewa, tun dama sojoji ba so suke su halaka shi ba, dalilin da yasa basu kai hari gidansa sai baya nan kuma su halaka jama’a
  • ’Dan ta’addan yace gwamnati tana son tunzura shi ne yayi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da yayi da gwamnatin jihar, hakan zai sa su halaka jama’a

Zamfara - Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, shahararren ‘dan ta’adda ne kuma shugaban ‘yan bindiga dake addabar jihohin Zamfara, Sokoto da Niger yace gwamnatin Najeriya bata da ra’ayin kawo karshen ta’addanci saboda wasu jami’an suna amfana daga shi.

Bello Turji
Gwamnati Bata Son Kawo Karshen Ta’addanci, Turji Ya Fallasa Masu Morewa Daga Rashin Zaman Lafiya. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Turji ya sanar da hakan matsayin martani ga luguden wutan da sojoji suke yi a gidansa kuma ya zargi gwamnatin da tunzurasu ta yadda har zasu karya yarjejeniyar zaman lafiya da suka yi da mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uwargidan Shugaban Kasa ta Huce, Ta Janye Karar Dalibin da ya ‘Zageta’

Turji a farkon shekarar nan ya jagoranci ‘yan kungiyarsa inda suka yi wa Zamfarawa kusan 200 kisan gilla har da mata da kananan yara.

A ranar 21 ga watan Augustan wannan shekarar, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Muhammad Hassan Nasiha, ya sanar da cewa Turji ya rungumi zaman lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma a ranar 18 ga watan Satumban, ya sha da kyar yayin da dakarun sojin saman Najeriya suka yi masa luguden wuta a gidansa dake kauyen Fakai na karamar hukumar Shinkafi ta jihar, lamarin da yayi sanadiyyar kisan mayakansa 12 da ‘yan uwa.

Hedkwatar tsaro ta kasa a ranar 14 ga watan Nuwamba ta ayyana nemansa da wasu ‘yan ta’adda 18 ruwa jallo inda ta saka kyautar N5 miliyan kan kowannensu.

A yayin martani kan luguden wutan da aka yi a gidansa, shugaban ‘yan bindigan ya zargin gwamnatin da karya alkawarin zaman lafiya da suka yi tare da baiwa jama’a kariya a yankin Shinkafi.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

A yayin zantawa da wani gidan talabijin na Hausa wanda Vanguard ta gani, Turji ya bayyana fushinsa kan ruwan wutan da ake yi a gidansa tare da halaka mutane marasa laifi bayan ya amince da jami’an gwamnati da shugabannin al’umma cewa zai bar ta’addanci.

A kalamansa:

“Ina mamaki idan da gaske gwmanati tana son halaka ni. Ina tunanin so suke su tunzura ni in karya alkawarin da na dauka ba cewa na daina kisa. Idan har zasu iya ganin gidana, me zai sai ba zasu ganni su halaka ni ba, saboda mintuna kadan na bar gidan kafin su yi ruwan wutan.
“Jama’a ya kamata su san makiyansu tun daga farko. Gwamnati tunzura mu take yi ta yadda zamu dauka fansa a kan talakawa.
“Gwamnati yaudarar jama’a take kan cewa tana son kawo karshen ta’addanci duk da cewa su ne ke hura wutar ta’addanci kuma suke mora daga ta’addancin.

Kara karanta wannan

Rikicin Rashin Albashi: ASUU Ta Sha Alwashin Balle Yajin Aikin da Ba a Taba Yi ba a tarihi

“Zaman lafiya yafi komai kuma ba shirya zama jakadan zaman lafiya sai dai idan gwamnati tana son mu cigaba da artabu. Na shiryawa zaman lafiya ko yaki. Duk abinda gwamnati take so, muna iya bata ninkin ta.”

Watanni 5 da suka wuce bamu kai hari ba, Turji

Kamar yadda yace:

“Watanni biyar da suka gabata ba a kai farmaki ba tun bayan yarjejeniya da muka yi da gwamnati amma yanzu sojoji suna kawo farmaki gidanmu. Muna jin kamar an ci amanarmu saboda rayukan da ake rasawa.
“Gwamnati ba nasarar tarwatsa wasu sassan gidana tayi ba kadai, har da gidajen wasu mutane wadanda basu ji ba, basu gani ba.
“A watanni biyar da suka wuce bamu hari kowa a Shinkafi ba. A saboda haka ne noma da sauransu kasuwanci suke cigaba. Ina matukar jin kunya idan aka kira sunana bayan farmakin wasu ‘yan ta’addan.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel