ASUU na Barazanar Balle Sabon Rikici kan Biyan Rabin Albashi

ASUU na Barazanar Balle Sabon Rikici kan Biyan Rabin Albashi

  • Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami’o’i suna barazanar sake balle sabon yajin aikin da ba a taba yi ba a tarihin jami’o’in Najeriya
  • Malaman sun bayyana hakan ne a taron da suka yi a jami’ar Ilorin wanda suka bayyana damuwarsu kan albashin rabin wata da aka biya su
  • A cewar kungiyar, malaman ba ma’aikatan wucin-gadi bane don haka zasu iya tarkata ayyukan da suka tarar su ki yin su saboda hakkinsu da aka rike

Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami’o’i, ASUU ta ankarar da ‘yan Najeriya kan cewa sabon rikici zai kunno kai wanda tace sai ya zarce wadanda aka taba yi a jami’o’in Najeriya, jaridar Daily Trust ta rahoto.

ASUU da Gwamnatin tarayya
ASUU na Barazanar Balle Sabon Rikici kan Biyan Rabin Albashi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Har zuwa yanzu, ASUU na neman dauki daga masu ruwa da tsaki tare da ‘yan Najeriya masu fadi a ji da su saka baki don Gwamnatin tarayya ta biya mambobinta a fadin kasar nan albashinsu da aka rike na tsawon wata takwas.

Kara karanta wannan

Karin Farashin Tikiti da Tsare-tsare da Za a Kawo a Jirgin Kasan Kaduna-Abuja

Shugaban ASUU na jami’ar Ilorin, Farfesa Mayosere Ajao, ya bayyana hakan a taro na musamman da aka yi a dakin taron jami’ar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, malaman jami’an sun fita zanga-zanga a cikin jami’ar kafin su koma dakin taron jami’ar inda suka yi jawabi ga manema labarai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace:

“Duk da mun koma bakin aiki a jami’armu, gwamnati tayi watsi da matsayarmu kan rike mana albashin wata takwas da tayi kan dogaro da tsarin babu aiki, babu biya. Hakan kuwa zai iya tayar da sabuwar kura.
“A kwanaki masu zuwa, kungiyar zata yi martani daidai da babu biya, babu aiki kuma zata bar ayyukan da suka taru na wannan lokacin da gwamnati take ikirari ta bakin Chris Ngige, cewa ma’aikatan basu yi aiki ba.”

Yace ana sanar da jama’a cewa sabon rikici na kunno kai wanda zai zarce duk wadanda aka taba yi a baya, kuma yace mambobin ASUU ba zasu cigaba da aiki kyauta ba.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana ‘Dan Takaran Gwamna, Mutane 26 Masu Harin Zuwa Majalisa Yin Takara

Ya kara da cewa:

“Kungiyarmu da mambobinta ba za a tuhumesu kan abinda matakin su zai janyo ba saboda martani ne kan halin mugunta da ake yi a Najeriya kuma zai shafi duk masu ruwa da tsaki.
“A matsayinmu na kungiya mai bin doka, mun saurari umarnin kotu wanda yace mu koma bakin aiki kafin a kammala shari’ar. Sai dai bayan dawowarmu, cike da mamaki gwamnati ta biya mu kudin rabin watan Oktoba.
“Ba zamu lamunci hakan ba kuma kungiyarmu ba zata aminta ba. A gaskiya a kan abinda ke faruwa shi ne mu ba ma’aikatan wucin-gadi bane. Ma’aikatan wucin-gadi ne kadai ake biya kan aikin da suka yi.”

FG ta biya malaman jami’a albashin rabin wata

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta biya malaman jami’a albashin rabin wata a farkon watan Nuwamban.

Hakan ya biyo bayan janye yajin aikin wata takwas da suka yi a ranar 14 ga wata ba Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel