Anga 'Ya 'Yan Buhari A Wajen Bikin Bude Yakin Neman Zaben Dan Takaraar Shugaban Kasa Na Jam'iiyar APC

Anga 'Ya 'Yan Buhari A Wajen Bikin Bude Yakin Neman Zaben Dan Takaraar Shugaban Kasa Na Jam'iiyar APC

  • Ba kasafai aka fiye ganin 'ya 'yan yan siyasa a wajen yakin neman zabe ko kuma gangamin siyasa ba a nigeria
  • A watan da ya gabata dan gidan Bola Tinubu, Seyi ya jagoranci wani maci a jihar kano don nuna goyan baya ga mahaifinsa
  • A ra'ayin 'yan Nigeria sa ahali ko dangi a siyasa wani abu ne da ke janyo alamun lamba a cikin gwamnatin ko makamancin haka

Katsina: Ya'yan shugaban kasa Muhammadu Buhari su biyu, Zahra da Hanan na cikin wasu fitattun mutane da suka bi sahun mata daga arewa maso yamma a Nigeria wajen kaddamar da yakin neman zaben Tinubu/Shettima a Katsina a jiya ranar Laraba. Uwargidan dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Remi Tinubu ta wakilci uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, wadda ita ce babbar uwar kungiyar yakin neman zaben mata na Tinubu da Shetima a wajen taron. Ta yi jawabi ga matan arewa maso yamma a dandalin a garin Katsina inda aka gudanar da bikin kaddamar da kamfen din.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

Sanata Remi ta godewa Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da al’ummar jihar Katsina bisa goyon bayan da suka nuna wa mijin nata tsawon shekaru, inda ta bada tabbacin cewa ba za su bar arewa ba a haka idan jam’iyyar ta ci zabe a 2023.

Zara hanan
Anga 'Ya 'Yan Buhari A Wajen Bude Yakin Neman Zaben Dan Takaraar Shugaban Kasa Na Jam'iiyar APC Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ta kuma yi addu’ar Allah ya baiwa Masari damar ci gaba da bayar da gudunmawar da za ta samu wajen kyautata rayuwar al’ummarmu na tsawon wasu shekaru masu zuwa, kamar yadda jaridar vanguard ta rawaito

“Ina so in tabbatar muku da cewa idan kuka zabe mu za mu kasance tare da ku, za mu zama abokin aiki dan ci gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu yi duk abin da ya kamata don ganin cewa arewa maso yamma, hatta arewa maso gabas sun samu zaman lafiya ," in ji Sanata Remi.

Kara karanta wannan

Abinda 'Yan Siyasar Mu Na Arewa Zasu Koya Daga 'Yan Kudu, Aisha Buhari

Su Waye Sukai Jawabi A nata bangaren, uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, Nana Shettima, wadda kuma ita ce ko'odinetan yakin neman zaben mata, ta yi kira ga matan shiyyar da su marawa Tinubu-Shettima baya a zaben 2023.

Har ila yau, da yake jawabi a wajen kaddamar da tuta, Gwamna Masari ya ba da tabbacin cewa al’ummar jihar Katsina za su tsaya tare da Tinubu har zuwa zabe.

“Bola Ahmed Tinubu yana gida tare da mu a jihar Katsina. kuma zamu bashi dukkan nin gudunmawa"
“Jihar Katsina gida ce ta APC kuma mun tsaya masa dari bisa dari. zamu bashi dukkan nin gudunmawa.” Inji Masari.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel