Aisha Buhari ta Janye Karar da Ta Kai na Dalibin da ya ‘Zageta’ a Soshiyal Midiya

Aisha Buhari ta Janye Karar da Ta Kai na Dalibin da ya ‘Zageta’ a Soshiyal Midiya

  • Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta janye karar dalibin da ta kai gaban kotu kan zolayarta da yayi a soshiyal midiya tare da saka hotonta
  • Lauyan masu gurfanar, Fidelis Ogbobe ne ya sanar da hakan a zaman kotun da aka yi a ranar Juma’a da ta gabata inda yace shigar ‘yan Najeriya masu fadi a ji yasa ta janye
  • Alkali Yusuf Halilu ya yabawa uwargidan shugaban kasan kan wannan matakin da ta dauka tare da kira ga iyaye da su dinga lura da lamurran yaransu

FCT, Abuja - Labarin dake zuwa da Duminsa a halin yanzu shi ne na janye karar Aminu Muhammad wanda uwargidan Shugaba Buhari, Aisha Muhammadu Buhari ta kai.

Aminu Muhammad da Aisha Buhari
Aisha Buhari ta Janye Karar da Ta Kai na Dalibin da ya ‘Zageta’ a Soshiyal Midiya. Hoto daga @bbchausa
Asali: Twitter

An cukuikuyi Aminu, dalibi a jami’ar tarayya ta Jigawa tun daga jihar har Abuja inda aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Dai Aminu Zai Gana Da Shugaba Buhari A Villa Yau, Bayan Aisha Buhari Ta Janye Karar Data Shigar

Lauyan Aminu, C.K Agu ne ya bayyana hakan ga BBC.

Muhammad wanda ya fito daga Azare ta jihar Bauchi, dalibin shekarar karshe ne a sashin kula da muhalli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano cewa ‘yan sanda sun damke dalibin bayan wata wallafa da yayi ta zolayar Aisha Buhari.

Wallafar wacce aka yi ta da harshen Hausa a watan Yunin 2022, tace:

“Sun mama an ci kudin talakawa an koshi.”

Wallafar Muhammad ta samu rakiyar hoton Aisha Buhari inda tayi jiki sosai.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, an gurfanar da Muhammad kan zargi daya a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Bayan sauraron karar, an aike Muhammad gidan gyaran hali.

A zaman kotun na ranar Juma’a, Fidelis Ogbobe, lauyan mai kara ya sanar da kotun cewa uwargidan shugaban kasan ta yanke hukuncin janye karar bayan ‘yan Najeriya masu fadi a ji sun shiga maganar.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

A yayin yanko sashi na 108 sakin layi na biyu na laifuka, Ogbobe ya mika bukatar janye karar.

A yayin yanke hukunci, Yusuf Halilu, alkali mai shari’a ya yabawa Uwargidan shugaban kasan kan wannan matakin da ta dauka na janye karar.

Yayin bayar da takardar sakin wanda ake zargi, Alkalin yayi kira ga iyaye da su kasance masu saka ido kan lamurran yaransu.

Ki yafewa ‘dan mu, Iyayen dalibin da ya zolaya Aisha Buhari sun yi roko

A wani labari na daban, iyaye ne Aminu Muhammad, dalibin da yayi wallafar zolaya ga Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, sun roketa.

A yayin bata hakuri, sun bukaci ta yafewa ‘dan su don basu san ya aikata wannan laifin ba sai bayan kwanaki biyar da aka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel