Bidiyon Yadda Amarya Ta Fashe da Kuka Ganin Yadda Tela Ta Gwangwaje Ya Jika Zukatan Jama’a

Bidiyon Yadda Amarya Ta Fashe da Kuka Ganin Yadda Tela Ta Gwangwaje Ya Jika Zukatan Jama’a

  • Bidiyon wata amarya Iruoma Ojika a shafin sada zumunta lokacin da take yaba tela ya ba da annashuwa a intanet
  • A bidiyon, an ga lokacin da amaryar ke sanye da kayan amarci tana zubar kwalla tana yaba alherin da tela ta yi mata
  • Jama’a da dama a kafar sada zumunta sun yi martani kan wannan bidiyon mai daukar hankali na cika alkawarin tela

Samun kwararren tela a kusa da kai a lokacin biki ba karamar nasara bace, watakila wannan yasa wata amarya ta shiga jazaba yayin da ta samu abin da take so.

A wani bidiyon da @asoebibella ta yada a kafar sada zumunta, wata amarya mai suna Iruoma Ojika ta shiga yanayin jin dadi mara misaltuwa da ganin kwarewar aikin telarta.

A bidiyon, an ga lokacin da amaryar ke sanye da wata tufa mai lauyin shudu da ta ja hankalin jama, wacce telar ta cancara mata ado, lamarin da ya taba zuciyarta.

Da take magana da telar mai suna Fatima, ta yaba mata, ta kuma gode da yadda ta cika alkawari kana ta yi mata fatan kada Allah ya hada ta da mugun rana a sana’arta ta dinki.

Cika alkawarin tela ya sa amarya ta fashe da kuka
Bidiyon Yadda Amarya Ta Fashe da Kuka Ganin Yadda Tela Ta Gwangwaje Ya Jika Zukatan Jama’a | Hoto: @asoebibella
Asali: Instagram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a game da bidiyon da aka yada

adaberrys_signature:

“Wannan abu akwai taba rai. Hakan na faruwa idan ka burge kwastoma fiye da tsammaninsa, za su sanya ka zama magajinsu. Tukuicin tela shine jin dadin wanda ya yiwa dinki. Allah ya yi musu albarka baki daya.”

jaydee_fabrics:

"Gaskiya ne wannan...wasu telolin daga sama aka turo su.”

gifteddemmyevents:

"Na gode da kika saka ta farin ciki a ranar mai muhimmanci a gare ta.”

ab_phylix:

"Telolin da suka dinka mana kaya da ya yi mana kyau muke yiwa addu’a suna kuka.”

ruqayyah.titi:

"Na duba shafinfa na ga kayan da dinka mata, kuma gaskiya wannan abin da ta jin da addu’ar duk sun cancanta.”

Budurwa ta rabu da saurayinta saboda ya nemi ta biya shi kudin maganin da ya siya mata

A wani labarin kuma, budurwa ta fasa auren saurayinta saboda ya nemi ta biya shi kudin maganin da ya siya mata a kan kudi N3k.

Wannan lamari ya ba wannan budurwa mamaki, har ta ce sam bata cancanci zama da mai rowa irinsa ba.

Jama'a sun yi martani, inda suka ce sam bai kyauta ba, ai soyayya akwai sadaukarwa da kula da juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel