Budurwa Ta Rabu da Saurayinta Bayan Ya Siyo Mata Maganin N3k Sannan Nemi Ta Biya Shi Kudinsa

Budurwa Ta Rabu da Saurayinta Bayan Ya Siyo Mata Maganin N3k Sannan Nemi Ta Biya Shi Kudinsa

  • Wata budurwa a TikTok mai suna Jackie Li ta bayyana yadda ta rabu da saurayinta saboda kudin da bai wuce N3k ba
  • Jackie ta bayyana cewa, saurayinta ya ba ta mamaki yayin da ta yi rashin lafiya duk da kuwa sun shafe shekaru hudu suna tare
  • A cewarta, saurayinta ya biya mata kudin magani N3k, amma daga baya ya nemi ta ba shi kudinsa kawai, bidiyon ya jawo cece-kuce

Wata budurwa a TikTok ta bayyana rabuwa da saurayinta da ta shafe shekaru suna tare saboda karamin dalili.

Budurwar 'yar Hawaii mai suna Jackie Li ta ce ta rabu da saurayinta ne saboda kudin da bai wuce N3k ba kacal.

A cewarta, wannan lamari na rabuwa da saurayin nata ya zo ne bayan da ya nemi ta biya shi kudin da ya ba ta ta siya magani a lokacin da ba ta da lafiya.

Kara karanta wannan

Sharrin GB Whatsapp: Matashi Ya Gano Budurwarsa Na Yi Masa Yankan Baya, Ya Fallasa Ta

Budurwa ta rabu da saurayinta saboda ya nemi ta biya kudin maganin da ya siya mata na N3k
Budurwa Ta Rabu da Saurayinta Bayan Ya Siyo Mata Maganin N3k Sannan Nemi Ta Biya Shi Kudinsa | Hoto: dailymail.co.u
Asali: UGC

A cewar rahoton Daily Mail, budurwar wacce ta kamu da ciwon sanyi ta aiki saurayinta da ya siya mata magani a shago, inda ya bukaci ta biya kudin maganin $7 ()N3k da ya kashe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda Jackie ta da saurayinta

A cewarta:

"Ina matukar halin rashin lafiya sai na tambayi saurayina a lokacin ko zai siyo min maganin sanyi a hanyarsa ta dawowa gida."

A wani bidiyon da ya shahara a TikTok, Jackie ta tuna yadda ta kwanta shirim ta kama bacci jim kadan bayan da saurayin nata ya kawo mata magani.

Ta ce ta sha mamaki ta kashe-gari ta tashi daga barci ta ga sakon tes daga saurayinta yana bukatar ta biya shi kudinsa.

Ta ce:

"Na tashi kawai naga ya nemi Vnmo su ja $7 na maganin."

Jackie ta kara da cewa, wannan lamari ya koya mata cewa, kawai za ta iya mu'amala ne da saurayin da bai damu da ta kashe masa kudi ko shi ya kashe mata ba.

Kara karanta wannan

Ta Sadu Da Tsohon Saurayi Tana Gab Da Aure, Bayan Wata 9 Ta Haihu, An Rasa Wanene Hakikanin Uban Yaro

Ta kuma bayyana dana-sanin shiga irin wannan alaka da saurayi mai son kai, amma ta ji dadin gano halinsa d akuma barin gaba daya.

Wannan labari da ta bayar ya ja hankalin jama'ar intanet da dama, inda suka bayyana cewa su za su iya siyan magani ga aboki ma haka siddan ba tare da neman biya ba.

Budurwa ta shirya auren saurayi, ta dauko fasto ta tafi dashi ofishin su saurayinta

Wasu kuwa sun bayyana mamakin cewa, basu taba jin labarin irin wannan saurayin ba

A baya kun ji labarin wata budurwa da ta dauko fasto musamman ta tafi zuwa ofishin da saurayinta ke aiki da nufin a daura musu aure.

Wannan lamari ya ba da mamaki, ganin yadda budurwar ta dage da nuna a hada ta zaman aure da saurayin nata.

Ana yawan samun lamuran da suka shafi rabuwa tsakanin saurayi da budurwa, hakan na da tasiri ga zamantakewa.

Kara karanta wannan

Yadda Girki Da Rubabben Tumatir Ya Yi Sanadiyar Da Saurayi Ya Rabu Da Budurwarsa, Jama’a Sun Yi Martani

Asali: Legit.ng

Online view pixel